"An dakatar da dukkan ayyukan gine-gine a yankin Agadem kuma an bai wa ma'aikatan wurin hutu har sai an inganta tsaro," in ji sanarwar CNPC. Hoto: Reuters

Kamfanin man fetur na ƙasar China ya dakatar da duk wasu gine-ginen da ake yi a cibiyar mai ta Agadem da ke gabashin Nijar bayan wasu hare-haren ta'addanci.

Dakatarwar dai na zuwa ne bayan wasu hare-hare da aka kai kan kayayyakin albarkatun man fetur a Nijar a 'yan watannin baya-bayan nan, ciki har da wanda 'yan tawaye suka yi ikirarin mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na Nijar da aka yi wa juyin mulki a bara.

Kamfanin man fetur na kasar China CNPC a ranar Laraba ya bayyana cewa, yanayin tsaro a wurin ya taɓarɓare bayan da "ƙungiyoyin 'yan ta'adda" suka kai “wasu hare-hare kan ayyukan man fetur” a ranar 12 ga watan Yuni.

"An dakatar da dukkan ayyukan gine-gine a yankin Agadem kuma an bai wa ma'aikatan wurin hutu har sai an inganta tsaro," in ji wata sanarwa da kamfanin CNPC ya fitar a ranar Lahadi wadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani.

Kamfanin na China ya ba da tabbacin cewa zai biya ma'aikatansa "albashin da ya dace daidai da adadin hutun" har sai yanayin tsaro ya inganta.

Har zuwa yanzu hukumomin mulkin sojan Nijar ba su mayar da martani kan matakin da kamfanin CNPC da ya zama babban abokin huldar Nijar ɗin tun bayan da aka fara haƙo mai a Agadem a shekarar 2011, ya ɗauka ba.

Harin "ta'addanci" kan cibiyar fetur mai muhimmanci

Cibiyar man fetur ɗin na da nisan sama da kilomita 1,700 (mil 1,056) daga Yamai babban birnin kasar, a yankin Diffa da ke gabashin hamada.

Ana fitar da ɗanyen mansa ne ta hanyar bututun mai da ya hada Nijar da ba ta da teku zuwa mashigin Tekun Atlantika na kasar Benin da ke maƙwabtaka da ita, wanda ‘yan tawaye da sauran kungiyoyin masu tayar da kayar baya suka kai wa hari.

Kungiyar Patriotic Liberation Front (FPL) da ke neman a maido da hamɓararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum bakin aiki, ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan bututun ne a daren ranar 16 ga watan Yuni "a matsayin gargadi na farko ga gwamnatin mulkin soja a Yamai".

Hukumomin sojan Nijar sun tabbatar da wannan aika-aikar da aka yi bayan shafe kwanaki da dama, inda suka bayyana shi a matsayin "ta'addanci" wanda aiki ne na "mugayen mutane".

Kuma a ranar 12 ga watan Yuni – a wannan rana ce CNPC ta ce an kai hari a filin mai na Agadem – inda aka kashe sojojin Nijar shida da ke ba da tsaro a wani hari na farko da 'yan fashi da makami' suka kai kan bututun mai a kudancin kasar, a cewar rundunar.

Baya ga hare-haren 'yan tawaye da na 'yan bindiga, ana kuma taƙaddamar diflomasiyya tsakanin Nijar da Benin a kan bututun man mai tsawon kilomita 2,000.

Ko da yake man bututun na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Nijar da na Benin, dangantakar da ke tsakanin Ƙasashen Yammacin Afirkan da ke maƙwabtaka da juna ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023.

A karkashin takunkumin da kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka ta ƙaƙaba mata kan korar Bazoum, Benin ta rufe kan iyakar kasar da Nijar.

Amma tuni Benin ta sake buɗe ɓangarenta na kan iyaka. Sai dai shugabannin mulkin sojan Nijar sun ƙi sake buɗe ɓangarensu "saboda tsaro" sun kuma katse kwararar mai ta bututun fetur ɗin.

Alkaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa, adadin man da Nijar take da shi ya kai kusan ganga biliyan biyu.

AFP