Wasu jiragen sama biyu sun yi karo da juna a Nairobi babban birnin kasar Kenya inda rahotanni suka ce an samu asarar rayuka. Hadarin ya afku ne a sanannen Gandun Daji na Nairobi kusa da filin jirgin saman Wilson.
Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Kenya ta ce hatsarin ya faru ne tsakanin wani jirgin sama na Makarantar Horon Koyon Tukin Jirgi ta Ninety-Nines da kuma jirgin fasinja na kamfanin Safarilink Aviation Limited a ranar Talata da safe.
Kafofin yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa jirgin na Makarantar Nine-Nines na ta shawagi ne domin samun horo yayin da ɗayan kuma na fasinja ne.
Hukumomin ba su bayar da cikakkun bayanai kan yawan asarar rayukan da aka samu ba da kuma abin da ya jawo hatsarin.
Amma kafafen watsa labaran cikin gida na rawaito cewa aƙalla mutum biyu ne suka mutu sannan wasu da dama sun jikkata.
Kamfanin Safarilink Aviation Limited na jiragen fasinja, ya ce akwai fasinjoji 39 da ma'aikata biyar a cikin jirgin da ya yi hatsarin.
Kamfanin ya ce jirgin na kan hanyarsa ta zuwa garin Diani da ke kusa da gaɓar teku ne, kuma jim kaɗan bayan tashinsa sai ya yi hatsari.
Hukumomi sun ce Sashen Kula da Hatsarin Jiragen Sama da Hukumar Ƴan sanda ta ƙasa sun fara gudanar da bincike a kan hatsarin.