Sudan na fama da rikici mai zafi tsakanin sojojin kasar da rundunar RSF tsawon wata guda inda kowannensu ke neman iko da kasar watanni 18 bayan juyin mulkin da aka yi.
Daruruwan mutane ne aka kashe kuma kusan mutum miliyan guda suka rasa muhallansu a yakin da ake yi tsakanin Shugaban Soji Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo wanda yake jagorantar RSF.
15 ga watan Afrilu: An soma rikici
A ranar 15 ga watan Afrilu aka soma jin karar fashewar bama-bamai a Khartoum. Rikicin ya zo ne kwanaki bayan da aka dage saka hannu kan yarjejeniya ta biyu kan mayar da mulki hannun farar-hula sakamakon rashin amincewar RSF na mayar da ita cikin rundunar sojin kasar.
Duka bangararen sojojin da kuma RSF sun zargi juna da soma kaddamar da hari kan juna.
RSF ta bayyana cewa ita ke da iko da filin jirgin Khartoum, da fadar shugaban Sudan da sauran muhimman wurare. Rundunar sojin kasar ta ce ta kai hari ta sama kan sansanonin RSF inda sojojin suka dage kan cewa su ke da iko.
Muhimman abubuwan da suka faru bayan hambarar da gwamnatin al Bashir
Haka kuma rikicin ya bazu zuwa yammacin Darfur – inda dama burbushin rikicin da ya samo asali ne tun daga 2003 – wanda ya kai ga kashe jami’an Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya.
Jagororin farar-hula a Sudan sun yi kira a tsagaita wuta, haka kuma Kungiyar Tarayyar Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Birtaniya da kuma wasu kasashen.
22 ga watan Afrilu: Saurin kwaso jama’a
A kwanakin da suka biyo baya, kasashen duniya sun yi ta saurin kwashe ‘ya’yansu daga kasar sakamakon yadda rikicin ke karuwa.
A ranar 22 ga watan Afrilu, Saudiyya ta zama kasa ta farko da ta sanar da cewa ta kwaso ‘yan kasarta daga Sudan.
Dubban mazauna Khartoum ne suka tsere wa rikicin kasar inda a kan hanya suka yi ta haduwa da gawarwaki da kuma motocin sojin da aka kona.
Sojojin Amurka sun kwashe jami’an diflomasiyyansu daga Khartoum. Daga baya sauran kasashe suka rika kwashe 'ya'yansu.
25 ga watan Afrilu: Saba yarjejeniya, ballewa daga gidan yari
An sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da dama amma babu wadda ta yi aiki. Amurka da kuma Saudiyya sun shiga tsakani kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 72 wadda ta soma 25 ga watan Afrilu.
Rundunar RSF da sojin kasar sun ta dage yarjejeniyar tsagaita wutar amma sun ci gaba da musayar wutar, inda duka bangarorin biyu ke zargin juna da sabawa.
A ranar, Ahmed Harun, wani jigo a lokacin mulkin Omar al-Bashir wanda aka kama da laifin take hakkin bil adama, ya sanar cewa ya gudu daga gidan yari tare da sauran wadanda aka kulle su tare.
Bashir, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya take nema kan zargin kisan kiyashi a yakin Darfur, tuni aka tura shi asibiti kafin aka soma rikicin, in ji rundunar sojojin Sudan.
Rikicin ya yi kamari a ranar 27 ga watan Afrilu a lokacin da jirgin yaki ya kai hari kan wuraren da RSF suke a Khartoum da kuma rikici da kuma sace-sacen da ake yi a Darfur.
A ranar 4 ga watan Mayu, Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa dole a “daina rikicin” inda kuma ya bayar da umarnin saka sabon takunkumi kan wadanda suke da hannu kan zubar da jinin.
5 ga watan Mayu: An kashe 750
Sama da mutum 750 aka bayar da rahoton cewa sun rasu tun bayan da aka soma rikicin, kamar yadda cibiyar tattara bayanai ta Armed Conflict Location and Event Data Project ta bayyana.
Wakili na musamman kan Majalisar Dinkin Duniya Volker Perthes ya bayyana cewa akwai wasu da suka shiga yakin daga Mali da Chadi da Nijar.
6 ga watan Mayu: Saudiyya ta yi magana
Tattaunawar da Amurka da Saudiyya suke jagoranta tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF a birnin Jeddah ba ta sa an tsagaita wuta ba, mako guda bayan tattaunawar.
A ranar 11 ga watan Mayu, duka bangarorin sun amince da za su bari a kai tallafi cikin gaggawa wuraren da ake rikici, “inda suka amince da kare farar hula”.
Majalisar Dinkin Duniya a ranar 12 ga watan Mayu ta bayyana cewa wannan rikicin ya jawo mutum 200,000 sun gudu daga kasar, inda adadin wadanda suka rabu da muhallansu ya kai kusan miliyan guda.