Mutane akalla 34 ne suka mutu sakamakon tashin gobara a wani defot ta man fetur da aka gina ba bisa ka'ida ba kudancin Jamhuriyar Benin kusa da kan iyaka da Nijeriya, a cewar wani jami'in gwamnatin kasar ranar Asabar.
"Wata mummunar gobara ta tashi a garin Seme Podji," in ji Ministan Harkokin Cikin Gida na Kasar Alassane Seidou a tattaunawa da manema labarai.
"Abin takaici shi ne mutum 34 sun mutu cikinsu har da jarirai biyu. Sun kone sosai saboda wutar da ta kama jikinsu sakamakon mu'amala da fetur din da aka yi fasa-kwaurinsa."
Ministan ya kara da cewa an kai mutum 20 asibiti inda ake jinyarsu, cikinsu har da wadanda suka samu munanan raunuka.
Yawancin masu kafa defot din suna yin fasa-kwaurin mai ne daga Nijeriya zuwa Benin inda suke sayarwa domin samun kazamar riba musamman bayan kasar ta cire tallafi a an fetur.