Sai da aka yi wa Itumeleng tiyata sama da 100 a lokacin tana karama. Hoto/Itumeleng

Daga Pauline Odhiambo

A lokacin da take jaririya ‘yar wata 11, Itumeleng Sekhu ta fado daga kan gado a Hammanskraal da ke Afrika ta Kudu inda ta fado wani kyandir ya fado a kanta. Sai wuta ta kama tsumman da aka lullube ta da shi inda har ta kai ga ya kona kayan da ke jikinta da haka kuma wutar ta soma kona jikinta.

Sai dai abin mamaki shi ne ba ta yi kuka ba. A lokacin da mahaifiyarta da kawunnanta suka ji kaurin hayaki daga wani daki, sai suka taho a guje domin su cece ta, zuwa lokacin Itumeleng ta kone sosai.

“A lokacin da mahaifiyata ta dauke ni, hannuna na dama na kan gado. Kunnena daya ya kone. Haka kuma na rasa yatsuna guda hudu da ke hannuna na hagu,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Sai da aka yi wa Itumeleng tiyata sau 104, inda wadda aka yi mata ta karshe ita ce lokacin tana shekara 15.

Ba lallai ne ba tabon da ke jininta da kuma wanda ke cikin zuciyarta su tafi, amma matar mai shekara 35 a halin yanzu tana zaune lafiya a yadda take bayan a baya ta sha fama da matsaloli na kaskantar da kai da kuma wasu matsaloli na lafiyar kwakwalwa.

“Ina da shekara tara a lokacin da wani yaro a ajinmu ya ce mani ina kama da konannen nama. Tun daga lokacin, ina kallon kaina a matsayin daliba mai kwazo a aji da karfin gwiwa,” in ji ta.

“A ko da yaushe ina sane da cewa wutar ta bar mani tabo, amma ban san yadda abin ya yi kamari ba sai da yaron ya fada mani wadannan kalaman.”

Itumeleng sai da ta yi yunkurin kashe kanta har sau uku. Hoto/Itumeleng

Wannan cin mutuncin ya jawo bakin-ciki da damuwa ta shekara 10 wadda ta bar tabo na abubuwa marasa dadin tunawa.

Dawowa daidai

Yayin da ta shiga cikin wani hali, Itumeleng ba ta san cewa neman taimako daga bangaren addini da kuma masu fadakarwa zai taimaka mata cire damuwa ba. Itumeleng sai ta tsunduma karatun littattafai daban-daban, ciki har da littattafan masu magana mai motsa rai, inda ta gano wani abu da ya sauya rayuwarta.

“Sai na gano kowane mutum a duniya yana da tabo. Nawa yana nunawa ne, amma da dama suna da tabon da ke cikinsu. Mutane da dama ba za su iya rabuwa da wadannan tabban ba saboda ba su da wadanda za su nuna mawa,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

“Sai na gano cewa na samu wadannan raunuka da tabban ne domin na zama wata hanya ta warkar da mutane.”

Sai a hankali manufarta ta sauya inda aikinta ya zama mai maganganu na bayar da kwarin gwiwa, wanda har hakan ta ja ta zama jakadiya ta musamman ga kamfanin Dove Unilever a 2015.

Tana tafiya zuwa makarantu da wuraren aiki da ke Afirka ta Kudu da sauran wurare domin karfafa gwiwar wasu.

Haka kuma ta kafa wata gidauniya mai suna Itumeleng Sekhu wadda ta yi aiki da makarantu 250, inda ta rinka samar musu da kayan karatu da kunzugu ga mata da ke Afirka ta Kudu.

“Maganganun da nake yi sun kai ni Kenya da Seychelles, wanda abu ne mai kyau saboda na yi kokari na bayar da kwarin gwiwa da yara maza da mata da dama kan matsalolin da suka shafi kaskantar da kai, da soyayya ga kawunansu da jagoranci,” kamar yadda Itumeleng ta bayyana wadda a halin yanzu take da ‘ya’ya uku.

Yadda duniya ke kallo

A 2014, Itumeleng ta rubuta littafi mai taken Me Kake Gani, wanda yake kalubalantar batun yarda da kai.

Itumeleng ta ce ta shafe shekara biyu tana rubuta littafinta. Hoto/Itumeleng

"Na dauki shekaru biyu kafin na rubuta littafina saboda dole ne in koma cikin tunanin da nake ji lokacin da nake so in kashe kaina.

Ba na son komawa can kuma, amma da na gama littafin, sai na gane cewa abin da ya kamata na yi ne a matsayin matakina na karshe na warkar da tabon da ke cikin zuciyata,” in ji ta.

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana, kashi 42 cikin 100 na rahotannin da ake samu daga fadin duniya na konewar yara ne.

Yawan mace-mace da konewa ke haifarwa a kasashe masu karamin karfi da matsakaita ya ninka sau 11 idan aka kwatanta da na kasashe masu samun kudin shiga, inda aka yi kiyasin mutane 43,000 ne ke mutuwa sakamakon kuna a nahiyar Afirka duk shekara.

Ana samun mutuwa shida ga kowane rukuni na mutum 100,000, wannan adadi ne mai ban mamaki.

Magance damuwa

Kamar yadda yake a cikin al'amarin Itumeleng, rukuni mafi rauni shi ne yara masu shekara ɗaya zuwa biyar.

Itumeleng ta soma yin kyandir domin magance tsoron da take yi wa kendir din. Hoto/Itumeleng 

Warkewa daga irin wannan damuwar na da hanyoyi daban-daban. A 2018, Itumeleng ta gano cewa akwai wani tabo guda daya da ya kamata ta rabu da shi – wato irin tsoron da take yi wa kyandir

“Ban taba kaunar kendir ba inda nake gudunsa, da sauran abubuwa masu zafi kamar gas da heater da rusho. Raina yana fadi mani cewa wadannan abubuwan za su iya lahanta ni a ko da yaushe, shi ya sa nake cikin tsoro a ko wane lokaci,” kamar yadda ta tuna.

“Ko yau, mahaifiyata ba ta amfani da kendir, ko rusho da heater, tana fama da raunin kwakwalwa kan abin da ya same ni.” Wata rana, Itumeleng ta tambayi kanta, “Tsawon wane lokaci zan ci gaba da rayuwa da wannan tsaron?”

Haskakawa

Ta gano cewa zama mai maganganu na bayar da kwarin gwiwa, zai zama abu mafi gamsarwa ga mutane don shaida musu su yi iya kokarinsu domin shawo kan fargabar da suke fama da ita.

Sakamakon yadda take da burin yin haka, sai ta shiga YouTube domin kallon hanyoyin da ake bi domin hada kyandir. “Na sha mamaki kan yadda na hada su – kan cewa zan iya yin wani abu mai kyau da hannu daya da yatsa daya.

Sai na samu sauyin tunani kan abin da ake nufi da haskaka rayuwar mutane ba tare da rage hasken tawa ba a lokacin da nake haskaka musu,” in ji ta.

Abin da na soma domin gwaji don na kawar da tsoro sai ya zama wani kasuwanci da nake yi tsawon shekara biyar. “Mun soma wani nau’in kyandir mai kyau. Yana da kyawun gani kuma kamshinsa na da dadi kuma kowa na so shi,” in ji Itumeleng.

“Ina kallon kaina a matsayin wadda konewa ta zamar wa nasara ba asara ba. Hakan ya faru ne sakamakon na san amfanina. Sanin dalilin da ya sa nake nan ya fiye mani konewar da na yi.

Kyandir ya yi kokarin lalata mani rayuwa, amma wannan kendir din a halin yanzu yana tare da ni kuma yana haskaka ni.”

TRT Afrika