Gamayyar kungiyoyin kwadago na Nijeriya karkashin babbar Kungiyar Kwadago ta kasar, NLC, ta amince ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin kasar a game da janye tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Kungiyar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Laraba da daddare bayan shugabanninta sun gana da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja.
Sanarwar, wadda shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na kungiyar TUC Festus Osifo suka sanya wa hannu, na zuwa ne kwana guda bayan sun soma zanga-zanga a fadin kasar bisa abin da suka kira tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na "kin jinin talaka".
“Mun yanke shawarar dawowa don ci gaba da sabuwar tattaunawa mai armashi saboda alkawarin da shugaban kasa ya yi" na duba wannan lamari, a cewar sanarwar.
Kungiyar ta kara da cewa ta samu sammaci daga kotu cewa ta raina hukuncin da ta yanke na hana ta gudanar da zanga-zanga tana mai yin kira ga 'yan Nijeriya da su sanya ido sosai domin kuwa "mulkin kama-karya" ya dawo.
Ranar Laraba da safe ne rassan kungiyar kwadagon a jihohi 36 da Abuja, babban birnin kasar suka tsunduma yajin aiki da zanga-zanga sakamakon janye tallafin mai wanda Shugaba Tinubu ya ce ba ya amfanar da galibin 'yan kasar sai wasu tsirarun 'yan damfara.
Sai dai hakan ya sa farashin fetur ya tashi inda ya kai fiye da naira 600, lamarin da ya shafi farashin kusan komai a Nijeriya sannan ya kara jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.
A makon nan shugaban ya ce kasar ta adana fiye da naira tiriliyan daya wata daya bayan janye tallafin, inda ya sha alwashin yin amfani da kudin wurin inganta rayuwar 'yan kasar kai-tsaye.