Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Legas da ke kudancin Nijeriya LASEMA ta ce ta ceto yara bakwai a wani gidan marayu da ya kama da wuta a jihar.
A sanarwar da hukumar ta LASEMA ta fitar a ranar Litinin, ta ce gidan marayun, wanda yake a yankin Aguda ya kama da wuta ne bayan na’urar sanyaya daki ko kuma iyakwandishin ta kama da wuta sakamakon matsalar wutar lantarki.
“Jami’an ceto na LASEMA sun ceto duka yara maza bakwai da ke wani gini mai hawa daya da ke dauke da marayu, wanda ya kama da wuta inda ta fara daga wata iyakwandishin da ke gidan sakamakon wutar lantarki.
“An kashe gobarar wadda a farko ta bazu zuwa dakin ajiye kayayyaki na gidan,” in ji sanarwar.
LASEMA ta kuma sanar da cewa an mika marayun a hukumance zuwa ga Mista Balogun da Mrs Rasheedat Sadik wadanda dukansu biyu Mataimakan Darakta ne a Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Al’umma ta Jihar Legas wadanda daga baya su ma suka mika su ga kungiyat Red Cross.
Haka kuma LASEMA din ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko kuma ya samu wani rauni sakamakon wannan gobara.