Janar Umaru Mohammed: An yanke wa Sojin Nijeriya hukuncin daurin shekara bakwai kan sata

Janar Umaru Mohammed: An yanke wa Sojin Nijeriya hukuncin daurin shekara bakwai kan sata

An kama Janar Umaru Mohammed da laifin satar sama da dala miliyan biyu da kuma sama da naira biliyan daya.
Kotu ta samu wanda ake zargin da laifuka 14 cikin 18 da ake zarginsa da su. Hoto/VON

Kotun Sojin Nijeriya da ke zama a Abuja ta yanke wa wani babban jami’inta Manjo Janar Umaru Mohammed hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai.

Shugaban Alkalan sojin wanda ya jagoranci zaman shari’ar, Manjo Janar James Myam ya samu babban sojin da laifuka 14 cikin 18 da ake zarginsa da su.

Kotun sojin ta bukaci Janar James ya mayar da dala 2,178,900 da kuma naira biliyan 1.65 ga Kamfanin Kadarorin Rundunar Sojin Nijeriya.

Laifukan da ake zarginsa da su sun haɗa da sama-da-fadi da kudade da kitsa tuggu da yin jabun takardu da karkatar da wasu kadarorin rundunar sojoji da kuma wasu sauran laifukan.

Labari mai alaka: Janar Umaru Mohammed: Za a yanke wa wani babban Janar na sojin Nijeriya hukunci kan almundahana

Kafin yanke hukuncin, Janar Mohamed na tsare a wani kwarya-kwaryan gidan yarin soji da ke Barikin Mogadishu a Abuja na wasu shekaru.

Lauyan da ke kare wanda ake karar Lekan Ojo ya bukaci a tura babban sojin da aka yanke wa hukunci zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje, sai dai alkalan na soji sun ki amincewa da hakan.

Manjo Janar Mohammed a baya ya kasance wanda ya jagoranci Kamfanin Kadarorin Rundunar Sojin Nijeriya.

TRT Afrika