Jami’a shige da fice na Ghana tare da taimakon jami’a kwastam sun kama wata babbar mota maƙare da jarkokin da aka cika da koko a kan iyakar ƙasar da ƙasar Togo.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ruwaito cewa bisa ga bayanan sirri ne jami’an suka yi wa babbar mota mai lamba AS 2103 da wani Ibrahim Fatawu ke ja kwanton-ɓauna.
Rahoton ya ce an yi kamen ne a ofishhin kan iyakar ƙasar na Ahve-Avi yayin da ake yunƙurin fasa-ƙaurin kokon zuwan ƙasar Togo.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato wata sanarwa daga jami’in hulɗa da jama’a na hukumar shige da ficen ƙasar Micheal Amoako-Atta tana cewa hukumar ta miƙa kokon da ta kama ga hukumar kula da harkar koko ta ƙasar.
“Hukumar shige da fice ta Ghana tana amfani da wannaa damar wajen yi wa duk mai niyyar fasa-ƙauri gargaɗin ya bari domin hakan yana mummunan tasiri kan tattalin arzikin Ghana tare da rasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati,” in ji sanarwar.
Ghana tana cikin ƙasashen da suka fi arzikin koko a duniya, sai dai kuma ba ta kai ƙasashen Turai irin su Switzerland cin moriyar kokon ba.
Ƙarin labari: Ghana ta kara farashin koko da sama da kaso 60