Al'adar bayar da ƙyauta ta Harambee a Kenya./ Hoto: TRT Afrika

Daga Dayo Yussuf

Tambarin Kenya, alamar ƙasar ce mai ban sha'awa wadda ke ɗauke da zakuna biyu riƙe da mashi da wata baƙa da ja da kuma koriyar fata ta gargajiya da aka ƙawata da zanen zakara mai riƙe da gatari.

Harambee ba kalma ba ce kawai, tana wakiltar wata al'ada da ta riƙe ƙasar Kenya wadda ke yankin Gabashin Afirka ta hanyoyi da dama.

Wani abu da ka iya dauke tunanin mutum daga wannan ƙayataccen tambarin shi ne kalmar da aka rubuta a ƙasan alamar ƙasar "Harambee," ma'ana "duk na ɗaya ne" a harshen Swahili.

Tarihin Harambee ya samo asali ne daga daɗaɗɗen tsarin rayuwar al'umma, inda a ƙa'ida ake fifita buƙatun al'umma fiye da buƙatun mutum ɗaya.

Wannan halayya ta yin kyauta da ba da gudunmawar gayya, sun taimaka wajen hada kan al'ummar Kenya har zuwa wannan lokaci, ba tare da la'akari da matsayin mutum ko ƙabilarsa ko kuma addininsa ba.

A wannan zamanin dai, Harambee yana nufin 'jama'a su tara kuɗi'- sai dai ma'anarsa da kuma tasirinsa ya wuce tara tsabar kuɗi kawai.

Bayan Kenya ta samu 'yanci daga bautar mulkin Birtaniya a shekarar 1963, sabbin shugabannin ƙasar suka soma amfani da Harambee a matsayin wani gangami na kira ga al'umma da su haɗa kai tare domin gina ƙasarsu tun daga tushe.

Jomo Kenyatta, wanda ya jagoranci miƙa mulkin, a matsayinsa na shugaban Kenya na farko, ya yi imanin cewa tasirin Harambee na iya taimakawa wajen samar da muhimman tsarin sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa a ƙasar.

Zamantakewa

Wannan kira, na aiki tare ya matuƙar taimakawa, kama daga tallafin al'umma wajen ba da kuɗi don a samar da asibitoci da tituna da filayen jama'a da za su amfani ko kuma tara kuɗi ga ɗaiɗaikun mutane waɗanda suke buƙatar taimako don biyan ƙudaɗin jinya mai yawa ko tura yara makaranta.

Gwamnatin Kenya ta haramtawa jami'anta ba da sadaqa a coci/ Hoto: Reuters 

''Tun daga lokacin da Kenya ta samu 'yancin kai, manufar Harambee shi ne a taimaka wa al'umma ta hanyar kawar da manyan maƙiyanta uku- talauci da cututtuka da kuma jahilci,'' in ji Farfesa Kennedy Ongaro, masanin ilimin zamantakewa kana malami a Jami'ar Dystar ta Nairobi.

'Yan ƙasar wadanɗa suke bin wannan tafarki tun bayan samun 'yancin kai a Kenya, sun bayyana yadda irin alfanu da kuma ci gaban da wannan tsari na haɗin kai da ke ƙunshe cikin al'adun Kenya ya samar wa ƙasar.

''Ni kaina na amfana da wannan tsarin na Harambee. Makarantar firamare da na yi an gina ta ne ta hanyar tara ƙuɗaɗe na Harambee, kuma an tura ni wata jami'a a ƙasar waje ta hanyar amfani da wannan tsari,'' in ji Farfesa Ongaro.

Tsarin na fuskantar matsala

Ɗaya daga cikin buƙatun da suka fito a lokacin zanga-zangar 'yan Gen Z kan dokar kuɗi a Kenya, shi ne a haramta wa jami'an gwamnati da shugabanni karɓar duk wani tallafin kudi daga jama'a.

Masu zanga-zangar sun yi nuni da cewa, wannan ɗabi'a da sunan Harambee ta zama wata kafa ta cin hanci da rashawa da shugabanni suke fakewa a kai wajen karkatar da kuɗaɗen da aka sace.

Wasu waɗanda suka yi imani ne suke karɓar kuɗaɗe a masallacin Omdurman na ƙasar Sudan/ Hoto: Reuters 

Jim kadan bayan haka ne, Shugaba William Ruto ya fito a wani gidan talabijin na ƙasar inda ya bayyana cewa za a yi sauye-sauye a harkokin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

Daga cikin sauye-sauye da ake shirin yi, ya ce gwamnatinsa za ta haramta tara kuɗaɗe da jama'a suke yi, musamman wanda ya hada da jami'an gwamnati.

Farfesa Ongaro na ganin, matakin zai zama tamkar rashin adalci ne ga al'ummar Kenya idan har aka kawar da wannan tsari mai fa'ida na Harambee.

'''Yan siyasa da masu fada a ji a cikin al'unmma suna yawo da jakunkuna cike da kuɗaɗe suna bayar da gudunmawar miliyoyin shillings a wuraren tara kudaɗe a fadin ƙasar, sai dai ba za su iya bayyana yadda ko kuma inda suka samu kuɗin ba,'' in ji shi

Kazalika attajirai da ke ba da gudunmawarsu don biyan wasu buƙatunsu su ma sun taka rawa wajen raunata imanin al'umma a ayyukan agaji.

Takaici game da yadda aka ɓata tsarin tara kuɗin al'umma ya fito fili ne a lokacin zanga-zangar. Lamarin da ya sanya Shugaba Ruto ɗaukar matakin korar kusan ɗaukacin majalisar ministocinsa.

Tuni dai ya sauya ministocin inda ya bar wasu tsoffin fuskoki daga cikinsu.

"'Yan Gen Z suna sane da yadda wasu cibiyoyi suke barin 'yan siyasa suna amfani da dandalinsu wajen ɓoye kuɗaɗen da aka sace sannan a fake da sunan bayar da gudunmawa,'' kamar yadda Farfesa Ongaro ya shaida wa TRT Afrika.

Ya bayyana rashin samar da tsari da kuma manufofin tafiyar da ayyukan Harambee a matsayin wani ɓangare na matsalar.

"Tun da babu wani taƙamaiman tsari na tafiyar da ayyukan, mutane suna samun damar yin duk abin da suka ga dama da sunan Harambee. Rashin gaskiyar tana kashe wa mutane gwiwa game da tasirin aikin,'' in ji malamin.

TRT Afrika