Matakan da gwamnatin kasar ta dauka a baya-bayan nan na daga cikin dalilan da suka jawo hauhawar farashi. Hoto/Getty Images

Masana a Nijeriya na ganin akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wurin ganin ta yi wa tufka hanci sakamakon yadda ake samun karuwar hauhawar farashin kayayyaki.

A ranar Litinin hukumar kididdiga ta Nijeriya ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar ta karu a watan Satumba zuwa matakin da ba a taba samu ba tsawon shekara 20 inda ya kai 26.72.

Haka kuma hukumar ta ce hauhawar farashin kayayyakin abinci zalla ta kai maki 30.64 a watan Satumba bayan an yi lissafi na tsawon shekara guda, idan aka kwatanta da yadda aka samu a Satumbar 2022 mai maki 23.34.

Sai dai ta ce amma an samu raguwar farashin abincin na wata-wata tsakanin Agusta zuwa Satumba da maki 1.41 inda a watan Agusta yana kan maki 3.87, amma a Satumba ya ragu zuwa 2.45.

Dakta Abdullahi Abubakar, Malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, ya bayyana cewa idan ana so a samu saukin wannan hauhawar farashin kayayyaki a kasar sai an daukaka darajar naira.

“Idan darajar naira ba ta daukaka ba, babu yadda za a yi kayan da ake shigowa da su su yi araha,” in ji Dakta Abdullahi.

Labari mai alaka: Dalilan da suka jawo sabuwar hauhawar farashin abinci a Nijeriya

Ya bayyana cewa Nijeriya ta kasance kasa wadda ta dogara ne da shigo da kayayyaki saboda haka idan canjin kudi ya y itsada ya zama dole komai ya yi tsada.

Dakta Abdullahi ya kuma ce matukar ana so a samu sauki akwai bukatar “gwamnati ta habaka tattalin arziki ta hanyar samar da duka kayayayyakin da ake amfani da su Nijeriya a cikin gida”.

Wannan hauhawar farashin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tsadar rayuwa a kasar. Adadin hauhawar da ake samu a watan Satumba na kayayyaki gama-gari ya ci gaba da karuwa a jere tsawon wata tara.

A watan Agusta matakin hauhawar farashin na kan maki 25.8, sai dai a watan Agusta ya kai 26.72 wanda hakan ke nufin cikin wata guda an samu karuwa da maki 0.92.

Hukumar ta ce makin hauhawar farashin ya karu ne sakamakon karin farashin kayayyakin abinci kamar man gyada da burodi da hatsi da dankali da doya da kifi da kayan lambu da nama da madara da kwai.

Ana ganin hauhawar farashin ba ya rasa nasaba da sabbin matakan tattalin arziki da gwamnatin kasar ta fito da su wadanda suka hada da cire tallafin man fetur da karya darajar naira da karuwar farashin makamashi.

TRT Afrika