Halilu Buzu: Rundunar sojin Nijeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban 'yan bindiga da take nema

Halilu Buzu: Rundunar sojin Nijeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban 'yan bindiga da take nema

Rundunar sojin Nijeriya ta yi kira ga mahukuntan Nijar da su kamo Halilu Buzu tare da hukunta shi kan abin da ya aikata.
Rundunar sojin ta ce ‘yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Buzu sun kashe mutum 19 a wani ƙauye a makon da ya gabata a wani hari da suka kai a Zamfara. Hoto: NA

Rundunar sojin Nijeriya ta nemi maƙwabciyarta Nijar da ta kama wani shugaban 'yan bindiga da ta ce tana nema ruwa a jallo a ƙasar. kamar yadda mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya faɗa a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Edward Buba ya ce Halilu Buzu ɗan ƙasar Nijar kuma shi ne babban mai samar da makamaki a Nijeriya daga masu sayar da su a Libiya.

A wata sanarwa, Buba ya ce Buzu yana kuma aiki a wani wajen haƙar zinare a Zamfara, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar satar mutane.

"A lokacin da dakaru suka kusa cim masa, sai ya tsallaka kan iyakar Jamhuriyar Nijar don neman mafaka," in ji Buba.

'Kama shi'

"A wannan lokacin, muna bi ta hanyoyin da suka dace dona kira ga hukumomin Nijar da su kama shi, tare da hukunta shi kan wannan ta'asa da ya aikata."

A watan Nuwamban 2022, sojojin Najeriya sun ce sun kashe Halilu Buzu tare da wasu shugabannin kungiyoyin masu garkuwa da mutane, amma Buba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis cewa "ba sabon abu ba ne a ce mutane daban-daban suna da suna iri daya ko da a tsakanin 'yan ta'adda."

Rundunar sojin ta ce ‘yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Buzu sun kashe mutum 19 a wani ƙauye a makon da ya gabata a wani hari da suka kai a Zamfara.

Yankin arewa maso yammacin Nijeriya ya shafe shekaru yana fama da matsalar ‘yan fashi, lamarin da ya yi sanadin kashe dubban mutane.

Reuters