Tattaunawar Habasha da Somaliland ta mai da hankali ne kan batun hadin gwiwar soji sakamakon takun sakar da ke tsakanin kasashen biyu kan yarjejeniyar amfani da tekun bahar maliya. / Hoto: Sojojin Habasha/Facebook  

Manyan dakarun sojin Habasha da na Somaliland, yankin da ya balle daga Somaliya sun yi wata ganawa a ranar Litinin a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kwamandojin sojin biyu sun tattauna batun hadin gwiwar sojin ne a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin gwamnatin Somaliya da ke Mogadishu, da gwamnatin Habasha.

Hakan na zuwa ne bayan an kulla yarjejeniyar farko tsakanin kasar Habasha wadda ta ba da gabar ruwa, da Somaliland a farkon wannan watan kan bukatar samun damar amfani da tashar jiragen ruwa ta tekun Bahar Maliya da ke Berbera a yankin na Somaliland.

A sanarwar da rundunar sojin Habasha ta fitar ta shafinta na Facebook a ranar Litinin, babban hafsan tsaro na rundunar sojojin kasar Habasha (ENDF) Field Marshal Birhanu Jula, da babban hafsan hafsoshin Soji na Somaliland Janar Nuh Ismail Tani, "sun tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen aiki tare kan hadin gwiwar soja.”

Kasar Somaliya ta yi watsi da yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da Habasha ta kulla da Somaliland, tana mai kiran hakan da "haramtaccen" mataki, sannan kuma barazana ce ga hakkin makwabtaka da kuma cin zarafi kan 'yancin-kan Somaliya.

Kazalika kasar ta yi wa jakadanta da ke Habasha kiranye bayan da aka sanar da yarjejeniyar.

Hanyar Bahar Maliya

Gwamnatin kasar Habasha ta kare matakin da ta dauka na sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da amincewar Mogadishu ba, tana mai cewa yarjejeniyarta da Somaliland ''ba za ta shafi wani bangare ko wata kasa ba.''

Yarjejeniyar ta bai wa Habasha damar samun wani sansanin sojin ruwa na dindindin, da kuma fannin hada-hadar ayyukan kasuwanci a mashigin tekun Aden.

Habasha ta yi asarar tashoshin jiragen ruwanta na Bahar Maliya a shekarun 1990 bayan yakin neman 'yancin-kai na Eritriya, wanda ya gudana daga shekarar 1961 zuwa 1991.

A shekarar 1991 ne Eritriya ta samu 'yancin-kai daga Habasha, wanda ya kai ga kafa kasashe biyu daban-daban.

Rabuwar ta sa Habasha ta rasa hanyar gabar ruwa ta isa Bahar Maliya kai-tsaye, da kuma manyan tashoshin jiragen ruwa.

TRT Afrika