Gwamnatin Rwanda ta sanar da haramta ayyukan ƙungiyoyi 43 na addini a faɗin ƙasar daga ranar 28 ga watan Agusta, makonni bayan ta rufe dubban coci-coci da aka buɗe ba bisa ƙa'ida ba.
Wata wasiƙa da Ma'aikatar Kula da Ƙananan Hukumomi ta ƙasar ta fitar ta umarci dukkan shugabannin gundumomi su tabbatar da aiwatar da wannan mataki, tana mai cewa bincike ya gano cewa ƙungiyoyin suna karya dokoki.
Galibin coci-cocin da lamarin ya shafa na da alaƙa da ɗarikar Pentecostal, ciki har da Cocin Lutheran, mamba a Gamayyar Cocin Lutheran na Duniya wadda aka buɗe a Rwanda a shekarun 1990 domin ci gaba da ayyukan Jamusawa 'yan mishan.
An sanar da haramta coci-cocin ne ranar Alhamis, makonni bayan hukumomi sun rufe fiye da coci 5,000 bisa zargin keta dokoki da jefa rayuwar masu ibada cikin hatsari.
Buƙatar bayar da horo
Hukumomi sun ce kashi 59.3 na coci 13,000 da aka gudanar da bincike a kansu a ƙarshen watan Yuli an rufe su saboda gaza bin doka.
Wannan ne karo na biyu da ake rufe coci-coci a ƙasar a shekarun baya bayan nan.
A shekara 2018, hukumomi a Rwanda sun rufe coci fiye da 700 da ake gudanarwa ba bisa ƙa'ida ba.
An umarci dukkan malaman coci su halarci wuraren bayar da horo kan addini kafin su buɗe coci kamar yadda doke ta tanada.
Gwamnati ta bai wa shugabannin coci-coci wa'adin shekaru biyar su aiwatar da matakan da ta tanada, sai dai rahotanni sun ce sau da dama sun gaza aiwatar da waɗannan matakai.