Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce za ta mayar da hankali wajen bunkasa fannin ilimin Nijeriya./Hoto:Bola Ahmed Tinubu.Facebook

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da amincewa da shaidar digiri na Jami'o'in kasashen Benin da Togo.

Ta dauki matakin ne bayan wata jaridar kasar ta wallafa rahoto da ya nuna yadda wakilinta da ya yi bad-da-kama ya samu digiri cikin kasa da wata biyu a wata jami'ar Benin.

“Wannan rahoton ya tabbatar da zargin da ake yi cewa wasu 'yan Nijeriya suna amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen samun shaidar digiri domin su samu ayyukan da masu digiri ne suke samu wadanda ba su kamata su samu ba," a cewar wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya Augustina Obilor-Duru ta fitar ranar Talata.

Ta kara da cewa “Ma'aikatar Ilimi ta Nijeriya tana yin tir da irin wannan aiki kuma daga ranar 2 ga watan Janairu na 2024 ta dakatar da amincewa da shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo har sai an kammala binciken da Ma'aikatun Ilimi na Nijeriya da kasashen biyu da kuma Hukumar tsaro ta DSS da Hukumar Kula da Masu yi wa Kasa Hidima, NYSC suke yi.”

Haka kuma ma’aikatar ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su taimaka wurin bayar da bayanai domin taimaka wa kwamitin neman mafita mai dorewa domin guje wa afkuwar hakan a gaba.

“Ma’aikatar ilimi na ta fama da matsaloli wadanda suka hada da na jami’o’in da aka bude ba bisa ka’ida ba a kasashen waje ko a cikin gida inda suke yaudarar ‘yan Nijeriya wadanda ba su ji ba su gani ba da kuma wasu ‘yan Nijeriyar da ke cikin bukatar mu’amula da irin wadannan wurare,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

An dade ana zargin cewa akwai wasu 'yan Nijeriya da suke zuwa wasu kasashen suna samo digiri cikin watanni.

Jami'o'in Nijeriya a 'yan shekarun nan sun shafe lokaci mai tsawo suna yajin aiki sakamakon wasu bukatu da suke neman gwamnatin Nijeriyar ta biya musu.

TRT Afrika