Dalibin da aka taba samu da laifin satar jarrabawa ba zai samu wannan bashin ba: Hoto/Jami'ar Bayero ta Kano

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka hannu kan doka domin kafa gidauniya ta musamman da za ta rinka bayar da bashi na musamman ga daliban kasar.

Da yake sanya hannu kan dokar ranar Litinin, shugaban kasar ya ce gidauniyar za ta saukaka wa daliban da ba su da hali na biyan kudin makaranta.

Ga dai wasu bayanai game da yadda daliban za su samu wannan bashi da kuma karin haske kan ayyukan gidauniyar:

  • Dole ne masu neman bashin su kasance sun samu gurbin karatu a jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha ko na ilimi ko na koyar da sana’o’in hannu wadanda gwamnatin tarayya ko jiha suka kafa.
  • Dole ne ka kasance ba ka da kudin da ya kai naira dubu 500 – kuma masu daukar nauyin karatunka ma ba su da shi.
  • Ya zama wajibi ka kawo mutum biyu da zasu tsaya maka wato gurantors: kuma dole su kasance ko ma’aikatan gwamnati da ke mataki na 12, ko lauyan da ya yi akalla shekara 10 yana aiki ko kuma ma’aikatan shari’a

Dalilan da za su hana bayar da bashi ga dalibi

Dalibi zai iya rasa damar samun bashi idan:

  • Ya taba saba alkawari a baya kan wani bashi da ya taba ci daga wata kungiya.
  • An taba kama shi yana satar amsa a yayin jarrabawa.
  • An taba kama shi da laifi a kotu ko kuma ya taba aikata wani laifi da ya shafi rashin gaskiya ko kuma zamba.
  • An taba kama shi da laifin shan miyagun kwayoyi; ko kuma -Iyayen dalibin sun taba gaza biyan bashi na karatu ko kuma wani bashi da aka taba ba dansu.

Yadda za ku nemi wannan bashi

Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wani dalibi da yake so ya amfana da wannan bashin ya zama tilas ya cika wadannan sharudan:

  • Dole ne dalibi ya saka takardar samun gurbin karatu a wasikarsa ta neman bashi.
  • Dole ne wandanda za su tsaya wa dalibin domin neman bashin su rubuta wasika ga shugaban kwamitin gidauniyar da ke bayar da bashin kuma a cikin wasikar su tabbatar da cewa su za su dauki nauyin duk wani abin da zai biyo baya idan dalibin ya ki biyan bashin.
  • Haka kuma dole ne dalibin ya kawo hotuna biyu na duka wadanda za su tsaya masa da shaidar suna aiki da kuma sunan ma’aikatar da suke aiki.
  • Idan wanda zai tsaya masa ba ya aikin gwamnati, dole ne dalibi ya kawo takardun rajista na kasuwancin mai tsaya masa idan ya yi rajista da hukumar da ke yi wa kamfanoni rajista da kuma bankinsa.

Karin bayani kan gidauniyar

Gidauniyar za ta rinka aiki ne a karkashin Babban Bankin Nijeriya hasali ma akwai kwamiti na musamman da dokar da ta kafa gidauniyar ta tanada wadda ta ce shugaban babban bankin zai kafa kwamiti da zai rinka saka ido kan ayyukan gidauniyar kuma shi zai jagoranci kwamitin.

Gidauniyar ita ce alhakin tantance daliban da bayar da bashi ya rataya a wuyanta. Haka kuma an ba ta karfin daukar duk wani mataki da ya dace kan dalibin da ya saba ko kuma ya gaza biyan bashin da aka ba shi.

Kwamitin da zai rinka saka ido kan ayyukan gidauniyar ya kunshi ministan ilimi na kasar da shugaban hukumar jami’o’in kasar da ministan ilimi ko wakilinsa da shugaban kungiyar malaman jami’o’i da jagororin kungiyar shugabannin kwalejojin kimiyya da na ilimi da jami’o’i har ma da wakilci daga kungiyar ASUU da dai sauransu.

TRT Afrika