Daliban Afirka da dama sun ce sun je Turkiyya karatu ne saboda labarai masu dadi da suka ji kan kasar/ Photo: AA

Daga Ebubekir Yahya

Zakiya Mabruck Mohammed, ’yar kasar Tanzaniya ce da ke karatun digiri na farko a fannin kimiyyar siyasa da gudanarwa a Jami’ar Ankara Yildirim Beyazit, ta dade tana sha’awar zuwa karatu Turkiyya.

“Na zo na yi karatu a nan a Turkiyya ne bayan samun bayanai masu kyau da kayatarwa daga abokaina wadanda suka riga ni zuwa kasar. Wadannan kyawawan bayanai ne suka sanya ni na nemi gurbin karatu ni ma.

“Asali ma dai yadda abokaina suka fada min yadda ’yan Turkiyya ke da karbar baki da girmama su ne ya sake kara karfafa min gwiwa.

"Na shaida hakan bayan na zo Turkiyya. Kuma zan bai wa duk wani dan kasar waje shawarar ya zo karatun nan kasar,” a cewar daliba Zakiya.

Tun bayan da kasashen Afirka suka fara samun ‘yancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka, Turkiyya ta fara kulla yarjejeniyar diflomasiyya da aiki tare da kasashen a bangarori daban-daban.

Turkiyya ta bude ofishin jakadancinta a Legas da ke Nijeriya a ranar 30 ga Agustan 1962, bayan shekaru biyu da samun ‘yancin kan kasar.

A watan Oktoban shekarar 1964 kuma Turkiyya ta bude ofishin jakadancinta a Accra, babban birnin kasar Ghana, shekara shida bayan Ghana ta samun cin gashin kanta.

Ya zuwa shekarar 2022 Turkiye na da ofisoshin jakadanci 44 a nahiyar Afirka. Wannan alaka ta diflomasiyya ta kawo kulla yarjeniyoyi tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka da dama a fannoni daban-daban.

Bangaren ilimi kusan shi ya fi haskawa a bangarorin da Turkiyya ta kulla alaka da kasashen Afirka.

Da fari Turkiye na bayar da tallafi ga daliban kasashen Afirka a karkashin yarjejeniyar aiki tare (Bilateral Agreement), amma daga baya da aka kafa Hukumar Kula da Turkawa da Danginsu da ke Kasashen Waje (YTB) a shekarar 2010, sai aka koma bayar da tallafin karatun a karkashin hukumar tare da sauran daliban kasashen duniya.

Farfesa Yunus Turhan na Sashen Nazarin Alakar Kasa da Kasa a Jami’ar Ankara Haci Bayram Veli, da ke babban birnin Turkiyya, ya bayyana yadda hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu a kasar suke bude kofofin zuwan daliban kasashen waje.

Ya ce “Tallafin karatu da hukumomin Turkiye irin su YTB da TIKA da ma kungiyoyi masu zaman kansu suke bai wa daliban Afirka ya kara sanya su zuwa Turkiyya sosai.“

A shekarar 2022, alkaluma sun bayyana cewa akwai daliban kasashen waje sama da 230,000 kuma daga cikin wannan adadi, sama da 15,000 suna karatu a karkashin tallafin hukumar YTB.

A jawabin da shugaban YTB Abdullah Eren ya yi a yayin taron yaye daliban da suka samu tallafi suka kammala karatuttukansu a 2022, ya ce a wannan shekarar sun yaye dalibai 2,325 da suka fito daga kasashen duniya 107.

Daliban kasashen Afirka da zabin zuwa Turkiyya

Duk da a tsakanin kasashen Kungiyar Hadin Kai kan Tattalin Arziki da Ci gaba, OECD, Turkiyya na mataki na 33 a alkaluman shekarar 2019 da aka fitar na yawan daliban kasashen waje.

Shugaban YTB Abdullah Eren ya ce a 2022 an yaye dalibai 2,325 da suka fito daga kasa 107/AA

Amma idan aka yi duba da kasashe masu tasowa sa’anninta, za a ga ta samu babbar nasara wajen bunkasa ilimi mai zurfi ta hanyar kara yawan jami’o’i da kwararrun malamai da samar da isassun kayan aiki da bincike da bayar da ilimi ingantacce da kuma karfafa alakarta da kasashen waje a fannin ilimi da tallafin karatu a matakai manya da kanana.

Dr. Aliyu Tilde kwararren masanin harkokin ilimi ne kuma tsohon Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi da ke arewacin Nijeriya, ya kuma yi wa TRT Afirka Hausa bayani kan dalilan da suka sanya dalibai daga kasar ke zuwa karatu Turkiyya maimakon sauran kasashen Turai.

Dr. Tilde ya fara da cewa ”Ai faduwa ce ta zo dai-dai da zama. Turkiyya da Nijeriya kasashe ne masu tasowa. Kuma mambobi ne na kungiyar kasashe takwas masu tasowa na D8.

“Sannan a al’adance ma a baya Turkiyya ce ta zama cibiyar Daular Usmaniyya. A lokacin ziyarar da shugaban kasar Turkiyya ya kai wa shugaban Nijeriya a 2016, an sanya hannu kan dangantakar taimakawa juna a bangarori daban-daban musamman a fannin ilimi. Duk wadannan abubuwa ne da ke kara bayar da karfin gwiwa.”

Farfesa Turhan na da ra’ayin cewa “Sakamakon yadda Turkiyya ke kara yaduwa a kasashen Afirka ne ya sanya daliban nahiyar ke son zuwa karatu Turkiyya. A shekaru 20 da suka gabata za a ga yadda Turkiyya ke kara habaka a kasashen Afirka.

Akwai jami’o’in Turkiye da suke sahun gaba a tsakanin manyan jami’o’i na duniya. Ya zuwa 2022 akwai jami’o’i 208 a Turkiye. Hoto: AA

“Hakan ya sanya ake samun karuwar daliban Afirka da ke zuwa Turkiyya karatu. Tare da hakan kuma, daliban da ke son zuwa Turkiyya karatu daga Afirka na yi wa kawunansu kallon kusanci da kasar saboda hadin kai a bangarori daban-daban,” in ji shi.

Masanin ya kara da cewa sauki da dadin rayuwa a Turkiyya ma wanda idan aka kwatanta da sauran kasashen gabashi sun sa ana rububin zuwa kasar karatu.

“Sannan wajen da Turkiyya take da kuma kasancewar ta kofar shiga Turai daga Gabas na kara sanya daliban Afirka zuwa kasar karatu,” kamar yadda Farfesa Turhan ya gaya wa TRT Afirka.

Akwai jami’o’in Turkiyya da suke sahun gaba a tsakanin manyan jami’o’i na duniya. Ya zuwa 2022 akwai jami’o’i 208 a Turkiyya. Jami’o’in sun hada da na gwamnati da masu zaman kansu.

“Sannan wajen da Turkiye take da kuma kasancewar ta kofar shiga Turai daga Gabas na kara sanya daliban Afirka zuwa kasar karatu.”

Farfesa Yunus Turhan na Jami’ar Ankara Haci Bayram Veli

Saukin kudi, samun manyan makarantu da tallafin karatu a Turkiyya.

Jami’o’in Turkiyya na da saukin kudin makaranta idan aka kwatanta da na kasashe makwabtanta ko ma wasu da dama na Turai.

Sannan ko a Turkiyyan ma, makarantun gwamnati sun fi masu zaman kansu sauki sosai.

Dr. Tilde daga Bauchin Nijeriya ya kuma kara jaddada wa TRT Afirka hakan inda ya ce ”Idan aka duba wasu kasashe irin su Ingila da Amurka da Jamus da sauran su, ka’idojin da suke gindayawa na daukar dalibai da bayar da biza na da tsauri sama da na Turkiyya.

"Idan mutum ya ga wadannan dalilai sai ya ga wato in dai da hali za ka gwammace ka je Turkiyya ka yi karatu.”

Dangantakar da Turkiye da Nijeriya suka kulla a 2016 a fannin ilimi ta taimaka sosai, in ji Dr Tilde/AA

Tsohon Kwamishinan na Ilimi na jihar Bauchin ya kuma bayyana saukin makarantun Turkiyya da zama daya daga cikin dalilan da suke sanya daliban kasashen waje zuwa don karatu mai zurfi.

”E nan ma akwai sauki sosai. Shi ne ma babban dalili kwarai da gaske. Na farko akwai jami’o’i kusan guda 60 a Turkiyya wadanda ’yan Nijeriya ke iya samun damar yin karatu kyauta babu ma zancen biyan kudin makaranta.

”Suna bayar da tallafin karatu cikakke ga dalibi. Ba zai biya kudin makaranta ba sai dai ya yi tanadin abin da zai ci da kuma sauran abubuwa irin su biza da gwamnati za ta nema”, in ji Dr. Tilde.

Kudin makaranta na shekara daya a makarantun gwamnati da daliban kasashen waje ke biya ba ya haura dalar Amurka 500, amma ban da nazarin likitanci.

Amma a makarantu masu zaman kansu, kudin na farawa daga dala 2,000 zuwa dubu 10 ga kwasa-kwasan da ba na likitanci ba.

"Idan aka duba wasu kasashe irin su Ingila da Amurka da Jamus da sauran su, ka’idojin da suke gindayawa na daukar dalibai da bayar da biza na da tsauri sama da na Turkiye. Idan mutum ya ga wadannan dalilai sai ya ga wato in dai da hali za ka gwammace ka je Turkiye ka yi karatu.”

Dr Aliyu Tilde, mai sharhi kan harkar ilimi a Nijeriya

Karatun likitanci a jami’o’i masu zaman kansu na farawa daga dala 15,000 zuwa dala 30,000.

Misali a kasashe irin su Jamu da, Ostireliya da Ingila da Holland da Amurka, dalibi na biyan kusan sama da dala 10,000 ko ma zuwa 15,000 domin karatun digiri na biyu a kowacce shekara.

A Turkiyya a makarantu masu zaman kansu, ana biyan kudin makaranta na digiri na biyu da na uku ne sau daya kawai, kuma har a gaba ba za a sake biya ba, amma kuma domin a saukakawa daliban, ana ba su damar biya a zangon karatu biyu ko uku.

Saukin rayuwa da girmama baki

Baya ga saukin makarantu a Turkiyya, wani abu da ke jan hankalin daliban kasashen waje shi ne yadda rayuwa take da sauki idan aka kwatanta da sauran kasashen Turai ko kasashe sa’anninta.

Dr Tilde ma ya sake kara haske kan yadda a Turkiyya ba a samun nuna wariyar launin fata ga daliban kasashen waje kamar yadda ake gani a kasashen Turai da Amurka.

Wanda wannan abu mai kyau da yake kara sanya wa mutane kaunar zuwa kasar don neman ilimi ga daliban kasashen waje.

Dalibai daga kasashen Afirka da dama kamar Habasha da Nijeriya da Kenya da Nijar ne ke karatu a Turkiye/AA

Shi ma a nasa bangaren, Farfesa Turhan ya bayyana saukin makarantun Turkiyya da ke bayar da ilimi mai inganci a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya daliban kasashen waje musamman na Afirka ke zuwa Turkiyya.

Ya kuma kara da cewa a Turkiyya babu nuna wariyar launin fata kamar yadda yake a kasashen Yamma.

Yasmin Aisha Ahmed ’yar Najeriya ce da ta yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Hacettepe da ke Ankara, kuma take kan yin digiri na uku a fannin lafiyar jama’a a Jami’ar Dokuzeylul da ke garin Izmir.

”Tabbas zan shawarci dalibai daga kasashen waje su zo karatu Turkiyya. Kudin makaranta da na biyan bukatun yau da kullum na da sauki sosai a Turkiyya idan aka kwatanta da wasu kasashen Turai.

Wannan dama ce da ba lallai sai ’ya’yan amsu hannu da shuni ne kawai za su zo karatu kasar ba.” in ji Yasmin.

Tun daga kudin hayar gida ko masaukin dalibai, kudin kashewa na yau da kullum da kudin abinci, ana samun sauki a Turkiyya fiye da kasashen Turai da ke makotaka da kasar.

Damarmaki ga daliban kasashen waje

Turkiyya ta samar da wani tsari don amfanin daliban kasashen waje. Bayan dalibi ya kammala karatunsa, ana ba shi izinin zama har na shekara guda domin neman aiki ko wasu damarmaki a kasar.

Ga daliban da suke da sha’awar aiki ko ci gaba da karatu, wannan tsari na taimaka musu matuka.

A lokacin da dalibai suke karatuttukansu, musamman masu karatun digiri na biyu da na uku, suna samun damar yin aiki a Turkiyya.

Wasu na koyarwa da yarukan da suka iya musamman Turanci a makarantun firamare da sakandire na Turkiyya. Wasu kuma na yin aiki a matsayin tafinta a kamfanunnukan kasar.

Baya ga wadannan, akwai damarmaki sosai ga daliban kasashen waje a Turkiyya wanda hakan ke kara sanya musu kaunar zuwa kasar neman ilimi.

A lokacin da dalibai suke karatuttukansu, musamman masu karatun digiri na biyu da na uku, suna samun damar yin aiki a Turkiyya. / Photo AA

Yasmin Aisha Ahmed ta kuma bayyana yadda ta samu tallafin Hukumar YTB ta Turkiye don yin karatuttukan nata.

”Abun jin dadi na samu nasarar samun tallafin karatu na gwamnatun Turkiye, wanda ya hada da kudin makaranta da wajen zama da inshorar lafiya da kudin kashewa a kowanne wata,” ta ce.

Baya ga wannan dama da Yasmin ta samu, ta kuma yaba yadda sashen kula da lafiya na Turkiyya yake da inganci da ma yadda manyan makarantun kasar suke horar da kwararru a fannin kiwon lafiya wanda hakan ke kara sanya ’yan kasashen waje zuwa neman lafiya.

”Tabbas zan shawarci dalibai daga kasashen waje su zo karatu Turkiye. Kudin makaranta da na biyan bukatun yau da kullum na da sauki sosai a Turkiye idan aka kwatanta da wasu kasashen Turai."

Yasmin Aisha Ahmed ’yar Najeriya mai karatu a Jami’ar Hacettepe da ke Ankara

Kasancewar yadda Turkiyya ta kulla kyakkyawar alaka ta kasuwanci da diflomasiyya da kasashen Afirka, na bai wa daliban da suka fito daga nahiyar damarmakin zama wata gada mai karfi tsakanin Turkiye da kasashen da suka fito.

Dalibai na samun damar aiki tare da ‘yan kasuwa da ke fitar da kayayyaki daga Turkiyya zuwa kasashen waje.

Daliban na taka muhimmiyar rawa saboda yadda suka iya yaren Turkanci da kuma yaren kasashensu da ‘yan kasuwar suke magana da shi.

A shekarar 2022 kawai, dalibai 165,691 daga kasashen duniya 171 ne suka mika takardunsu don neman tallafin karatun gwamnatin Turkiyya.

Turkiyya za ta ci gaba da zama cibiyar daliban kasashen waje musamman ma na Afirka saboda kyakkyawar alakar kasar da kasashen waje da ingantattun jami’o’i da saukin kudin makaranta da na rayuwar yau da kullum.

Turkiyya kasa ce da ke zama wata gada tsakanin Gabas da Yamma!

TRT Afrika