Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta tabbatar da dawo da bayar da tallafin karatun digiri na biyu ga ‘yan jihar.
Gwamnatin Jihar ta wallafa bayanai kan tallafin a shafinta na intanet inda ta ce ‘yan asalin jihar ne kadai za su amfana da wannan tallafin.
“Bayan shekara takwas ba tare da gwamnatin baya ta bayar da tallafin karatun digiri na biyu na kasar waje ba, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da dawo da bayar da tallafin karatun kasar waje da cikin gida daga zangon karatu na 2023/2024,” in ji sanarwar da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sharuddan samun tallafin
- Dole ne mutum ya zama dan asalin jihar Kano.
- Sai mutum ya kammala digirinsa na farko da sakamako mafi kyawu wato First class. Sa’annan kuma dole ne jami’a ko kuma kwalejin da mutum ya samu digirinsa ta kasance an amince da ingancinta.
- Haka kuma akwai bukatar wanda za a bai wa tallafin ya kasance yana da cikakkiyar lafiya da zai iya tafiya wani wuri ya kuma iya yin karatun.
- Dole ne mai neman wannan tallafi ya cike fom din neman gurbin tallafin wanda aka saka a shafin intanet na gwamnatin jihar.
Yadda za a nemi tallafin
- Bayan cika sharuddan da gwamnatin jihar ta bayar, mataki na gaba shi ne cike fom din neman gurbin tallafin.
- Za a iya shiga wannan shafin www.kanostate.gov.ng/scholarship_application domin sauke fom din sai a cike shi cike.
- Bayan cike fom din, za a hada shi da takardun karatun makaranta da suka hada da takardar shaidar zama dan jiha da takardar asibiti da ke nuna mutum yana da koshin lafiya da takardar haihuwa da takardar karatun firamare, da takardar WASC ko GCE ko SSCE da kuma takardar digiri ko matakin karatu da ke daidai da digiri.
- Za a kai duka wadannan takardu sakateriyar kwamitin tantance wadanda suka cancanta da ke tsohon dakin taro na ofishin sakataren gwamnatin Kano, gini mai lamba 1 Wudil Road Kano.
- Dole ne a kai wadannan takardun cikin makonni biyu bayan da aka fitar da wannan sanarwa.
A shekarun baya dai gwamnatin ta Kano ta sha bayar da tallafin karatu ga ‘yan jihar inda tuni wasu suka zama likitoci da injiniyoyi da matukan jirgin sama duk da tallafin na gwamnati.
Gwamnatin ta Kano ta ce tallafin karatu na karshe da aka bayar a jihar an bayar da shi ne a lokacin Sanata Rabiu Kwankwaso yana gwamna inda ya dauki nauyin dalibai 503 domin su yi karatu a kasashe 14.