Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta dakatar da tashar Canal 3 tsawon wata guda a ƙasar.
Ministan Watsa Labarai na Nijar Mohamed Raliou ne ya sanar da dakatarwar a wata dokar soji da ya karanto a ranar Juma’a 17 ga watan Janairun 2025.
Haka kuma gwamnatin ta Nijar ta janye lasisin babban editan tashar talabijin ɗin wato Seini Amadou tsawon watanni uku, kamar yadda kafar watsa labarai ta ActuNijar ta ruwaito.
Gwamnatin Nijar ta ce ta dakatar da tashar ta Canal 3 ɗin ne sakamakon saɓa wasu ƙa’idoji na watsa labarai da ta yi, sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan ainahin laifin da ake tuhumar tashar da aikatawa ba.
Sai dai ana ganin dakatarwar da aka yi wa tashar ba ta rasa nasaba da wani shiri na musamman da aka gabatar a tashar inda aka yi sharhi game da ministocin gwamnatin mulkin sojin ƙasar tare da zayyano waɗanda suka yi ƙoƙari da waɗanda suka ɗan kamanta da kuma waɗanda ba su yi aiki sosai ba.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta saka takunkumi ga kafofin watsa labarai ba.
Ko a kwanakin baya sai da ta dakatar da watsa shirye-shiryen BBC da kuma maka gidan rediyon Faransa a kotu saboda zargin watsa labaran ƙarya.