An amince da Nijeriya a matsayin “abokiyar hulɗa” ga ƙasashen BRICS, kamar yadda Brazil wadda ita ce jagorar ƙasashen ta bayyana.
Ƙasashen Brazil da Rasha da India da China ne suka kafa BRICS a shekarar 2009, inda a 2010 aka saka Afirka ta Kudu a ciki, inda ake ganin an kafa ta domin takara da ƙasashe bakwai mafi ƙarfin tattalin arziƙi.
A bara, ƙasashen sun saka Iran da Masar da Habasha da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa a cikin ƙungiyar.
Haka kuma ƙungiyar ta gayyaci Saudiyya domin ta shige ta. Ƙasashen Turkiyya da Azerbaijan da Malaysia a hukumance sun aika da buƙatarsu ta zama mambobi, haka kuma akwai wasu ƙasashen da su ma suka nuna sha’awarsu.
Nijeriya ce ƙasa ta tara da ta zama abokiyar hulɗar BRICS bayan Belarus da Bolivia da Cuba da Kazakhstan da Malaysia da Thailand da Uganda da Uzbekistan.
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump a bara ya yi barazanar ƙara haraji da kaso 100 bisa 100 ga ƙasashen BRICS idan suka yi wa dalar Amurka zagon ƙasa.
Sai dai ƙasashen sun sanar da aniyarsu ta fitar da sabuwar hanyar biyan kuɗi ba tare da dogara da dalar Amurka ba.
Amincewar Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya a nata ɓangaren, ta amince da gayyatar da ƙasashen na BRICS suka yi mata domin ta zama abokiyar hulɗar su.
“Amincewar a hukumance domin zama ƙasa abokiyar hulɗa ya nuna muhimmancin sadaukarwar Nijeriya wurin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasa da ƙasa, da amfani da damarmaki na tattalin arziƙi da kuma ƙara haɓaka dangantaka wadda za ta zo daidai da muradun ci gaban Nijeriya,” kamar yadda sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta bayyana.
Nijeriyar ta kuma bayyana cewa a matsayin BRICS na manyan ƙasashe da tattalin arziƙinsu ke haɓaka a duniya, zamansu abokan juna zai ƙara bai wa Nijeriyar damar kasuwanci da zuba jari da haɗin kai da sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar.