A madadin Turkiyya, Utkan ya mika sakon ta'aziyya ga Chadi sakamakon harin da aka kai kwanaki a fadar shugaban kasa da ke babban birnin N'Djamena. / Hoto: Abokan hulda

Babban jami'in diflomasiyyar Chadi da ke Tsakiyar Afirka ya karbi bakuncin jakadan Turkiyya inda suka tattauna kan hadin kan kasashensu.

A yayin ganawar tasu a ranar Alhamis, Ministan Harkokin Waje Abderaman Koulamallah da Jakadan Turkiyya Cem Utkan sun mayar da hankali kan muhimman bangarori kamar tattalin arziki, kasuwanci, ayyukan noma, makamashi da raya al'adu, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

Sun tattauna kan hanyoyin karfafa alakar kasuwanci ta hanyar zuba jarin Turkiyya a Chadi.

Bangarorin biyu sun kuma yi duba ga kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin da hanyoyin hadin kai.

A madadin Turkiyya, Utkan ya mika sakon ta'aziyya ga Chadi sakamakon harin da aka kai kwanaki a Fadar Shugaban Ƙasa da ke babban birnin N'Djamena.

A ranar 8 ga Janairu aka kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi inda aka yi artabu tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga.

A yayin harin, an kashe 'yan bindiga 18 da jami'in gwamnati guda.

Ofishin Jakadandin Turkiyya a N'Djamena ya tabbatar da ganawar a wata gajeriyar sanarwa da ya fitar ta shafin X wadda ke cewa bangarorin biyu sun tattauna kan hadin kansu da ma al'amuran kasa da kasa.

TRT World