Gwamnatin Ghana ta sanar da cewa za ta samar da wani kamfani da kuɗinsa ya kai kimanin dala miliyan 450 domin sarrafa sinadarin manganese da aka samar a ƙasar.
Haka kuma ƙasar ta ce za ta haramta fitar da sinadarin bauxite idan majalisa ta amince da dokokin da ke gabanta na ma’adinai.
Haka kuma gwamnatin ƙasar ta ce za ta bayar da fifiko ga masu zuba jari ƴan asalin ƙasar Ghana waɗanda suke so su mallaki wurin haƙar ma’adinai na uku mafi girma a ƙasar na Newmont Corporation – wato wurin haƙar ma’adinai na Akyem da ke Yankin Gabashi.
Shugaban na Ghana Nana Akufo-Addo ya ce wannan yunƙurin da ake yi duka ana yin sa ne domin tabbatar da cewa an samu kuɗi a ƙasa da kuma haɓaka tsarin da gwamnatin ƙasar ta fito da shi na ƙarfafa masana’antu.
Shugaban ya bayyana duka waɗannan ne a lokacin da yake jawabi dangane da halin da ƙasar take ciki a ranar Talata.
Shugaban na Ghana ya ƙara jaddada cewa a bara, Ghana ta ƙara samun matsayinta na ƙasar da ta fi samar da zinare a Afirka, inda ta samar da oza miliyan huɗu , wanda hakan ya sa ta sha gaban Afirka ta Kudu.
Haka kuma shugaban ya bayyana cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wurin kiyaye dazuka da namun dajin ƙasar.
Ya ce sakamakon haka ne ma gwamnatinsa ta shuka bishiyoyi miliyan 42 a cikin shekaru uku da suka gabata a ƙarƙashin shirin Green Ghana Project, inda kuma aka girbe kadada 690,000 tsakanin 2017 zuwa 2022.