Ƙarin kuɗin wuta da ruwan zai fara ne daga watan Yulin bana. / Hoto: Getty Images

Hukumar da ke kula da kamfanonin da ke samar da ababen more rayuwa na Ghana PURC ta sanar da cewa daga Yulin bana, za a yi wa ‘yan ƙasar ƙarin kuɗin lantarki da ruwa.

Hukumar ta ce za a yi ƙarin kashi 3.45 cikin 100 ga ƙananan kwastamomi masu amfani da wuta daga kilowatt 0-30, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito.

Haka kuma hukumar ta ce ta yi ƙrin kashi 5.84 cikin 100 ga sauran masu gidaje da wuraren kasuwanci masu amfani da wuta daga kilowatt 31 zuwa sama.

Ga waɗanda ke a rukunin kamfanoni kuwa, hukumar ta yi musu ƙarin kashi 4.92cikin 100.

PURC ta ce duka wannan ƙarin zai soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Yulin bana. Ga kuma masu amfani da ruwa, za a samu ƙarin kashi 5.16 ga duka kwastamomi da ke kan kowane rukuni.

Ana sa ran wannan ƙarin zai yi aiki tun daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga watan Satumba.

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ƙarin kuɗin lantarkin da na ruwan ne sakamakon wasu matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashin dala a ƙasar da tsadar man fetur da gas.

TRT Afrika