Jihar Katsina na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro a Nijeriya. / Hoto: Dikko Radda

Gwamnan Jihar Katsina ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan nasarar da suka samu wurin kashe ‘yan ta’adda 80 a jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Katsina Dakta Nasir Muazu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda kwamishinan ya ce sojojin sama na Operation Fansan Yamma da sojojin 17 Brigade da ‘yan sanda da DSS da kuma jam’ian sa kai na Community Watch Corps and Vigilantes ne suka gudanar da wannan aikin a ranar 4 ga watan Janairun 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun kai samame sansanonin ‘yan bindiga da ke a Kadoji da Matso-Matso da Bagga da Dogon Marke da Takatsaba da ke yankin Jibia.

“Wannan farmakin da aka gudanar a ranar 4 ga watan Janairun 2025, ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna an kafa sansanonin ‘yan bindiga a kewayen karamar hukumar, lamarin da ya kara ta’azzara ayyukan ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da Batagarawa,” in ji sanarwar.

“Aikin haɗin gwiwar sojojin sama da ƙasa ya yi sanadin kashe ‘yan bindiga 80, tare da jikkata wasu da dama. Haka kuma, an lalata maɓoyarsu da muhimman wuraren gudanar da ayyukansu, lamarin da ke nuna babbar illa a gare su.”

Kashe jagoran ‘yan bindiga a Tsafe

Hakazalika Sojojin Operation Fansan Yamma a Jihar Zamfara a ranar 4 ga Janairu sun yi arangama da ‘yan ta’adda a ƙauyen Bamamu a Ƙaramar Hukumar Tsafe da ke Zamfara.

A yayin arangamar, sojojin sun kashe Sani Rusu, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta Operation Fansan Yamma Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar.

Haka kuma ya bayyana cewa sojojin sun ƙwato makamai a wani hari da suka kai na daban a Kwanar Jollof da ke Shinkafi inda suka kashe wasu ‘yan ta’adda da ƙwace makamai da babura.

Kashe shugaban Miyetti Allah a Katsina

Sai dai nasarar da jami’an tsaron suka samu na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka kashe shugaban riƙo na ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Katsina Alhaji Surajo Amadu Rufa’i.

‘Yan bindigar sun kashe shi ne a gidansa da ke ƙauyen Marina a Ƙaramar Hukumar Kusada.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da lamarin inda ya ce bayan sun kashe Rufa’i, sun yi garkuwa da matarsa da ‘yarsa.

TRT Afrika