Ministan harkokin wajen Guinea ya shaida wa jami'an diflomasiyya cewa tsaikon da ake samu a kan intanet a kasar na faruwa ne saboada wata "matsalar tsaro", a wani jawabin da aka watsa a gidan talabijin na kasar.
Kimanin jakadun kasashe 15 ko wakilansu ciki har da wakilai daga kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da China ne suka gana da Morissanda Kouyate domin kokawa kan rashin ingancin intanet, kamar yadda jawabin da aka watsa ranar Laraba da maraice ya nuna.
Sun koka a kan keta 'yancin fadar albarkacin baki da rashin samun intanet da rashin man fetur bayan an yi mummunar gobara a babban wurin ajiyar fetur a ksar a watan Disamba da kuma matsalolin da ke fuskantar ma'aikatansu.
An kwashe makonni ana fama da matsanancin rashin intanet a Guinea, wadda sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 2021 suke mulka.
Matsaloli masu yawa
Mahukunta kuma sun sanya sharudda kan kafafen watsa labarai masu zaman kansu yayin da aka katse kafafen sada zumunta da kuma gidajen rediyo masu zaman kansu tare da shafukan intanet na jaridu sannan ake kamawa ko far wa 'yan jarida.
"Ta shafi dukkanmu, wata matsalar tsaro ta shafe mu," in ji Kouyate a cikin jawabin da ya yi a talabijin.
Bai ba da karin bayani ba game da matsalar. "Ba za mu iya kara bayani a kai ba," in ji shi.
Ministan na harkokin waje ya kuma shaida wa jami'an diflomasiyya cewa matsalolin da ofisoshin jakadancinsu ke funkanta sun shafi ma'aikatan kasar Guinea ma.
'Ta shafi' fadar shugaban kasa
"Game da matsalar sadarwa, akwai wannan matsalar a fadar shugaban kasa," a cewarsa, yana mai karawa da cewa za su warware matsalar nan ba da jimawa ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta koka a karshen watan da ya gabata game da "karuwar take 'yancin 'yan jarida " a Guinea kuma ta yi kira ga hukumomi su sauya yanayin nan-take.
Kanar Mamady Doumbouya, shugaban gwamnatin mulkin soja ta kasar, ya yi alkawarin mika mulki ga farar-hula a watan Janairun shekarar 2026.