Gasar cin kofin sada zumunci tsakanin Turkiyya da Sabiya ta kasance wata al'ada da Belgrade babban birnin kasar Sabiya ya saba yi tun 2018.
A wannan karon an gudanar da gasar ne don taimaka wa mutanen da iftila’in tagwayen girgizar kasa da ta auku a Turkiyya ta rutsa da su a farkon watan Fabrairu.
‘Yan kulob din tsaren kekuna da ke Mardin a Turkiyya, daya daga cikin biranen da iftila’in girgizar kasar ya yi barna, sun kasance manyan baki na musamman a wajen gasar da aka yi a ranar Lahadi, inda sama da masu tuka keke 250 suka halarta.
Jakadan Turkiyya a Sabiya Hami Aksoy, ya ce sun kuma yi bikin ranar samun 'yancin kai da yara da kuma bikin cika shekara 103 da kafuwar Majalisar Dokokin kasar.
"Wasa yana hada kan al’umma, da tara su wuri daya. Za mu ci gaba da irin wannan ayyukan in ji Aksoy."
Kyakkyawar Dangantaka
Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wasanni ta kasar Serbia Marko Keselj, ya ce ya yi farin ciki da cewa wannan wata dama ce da kuma lokaci na karfafa ‘yan uwantaka da abokantaka a tsakanin kasashen biyu.
"Bayan mummunar iftila'in girgizar kasa da ya afku a Turkiyya, masu aikin ceto daga Sabiya da Ma’aiktan kashe gobara na daga cikin wadanda suka fara kawo dauki ga mutanen Turkiyya.
Don haka wannan tsaren da sauran wasannin motsa jiki za su iya zama wasu misalai ga yadda muke karfafa kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin kasashenmu,’’ in ji Keselj.
Jama'a da kungiyoyi masu zaman kansu na fararen hula har da gwamnatin kasar Sabiya sun yi ta hada gangami don taimaka wa wadanda girgizar kasa a Turkiyya ta shafa.
Tagwayen girgizar kasa da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu a kudancin Turkiyya ya yi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 50,000 a kasar.
Karfin girgizar kasar da ya kai maki 7.7 da kuma 7.6 ya afku ne a larduna 11 na Turkiyya, wadanda suka hada da Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da kuma Sanliurfa.
Kimanin mutum miliyan 14 ne girgizar kasar ta shafa a Turkiyya.