Hukumomi a Maroko ranar Asabar sun ayyana makokin kwana uku a fadin kasar bayan mummunar girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 1,000, a cewar wata sanarwa daga fadar sarkin kasar.
"An ayyana makokin kwana uku na kasa baki daya, inda za a sauko da tutocin kasar kasa-kasa a dukkan gine-gine gwamnati," in ji sanarwar da kamfanin dillacin labarai na MAP bayan Sarki Mohammed VI ya jagoranci wani taro da ya tattauna kan wannan bala’I da ya fada wa kasar.
Girgizar kasar ita ce mafi girma da kasar ta taba fuskanta, inda ta fi yin barna a birnin Marrakesh mai dimbin tarihi.
Hukumomi sun tabbatar a mutuwar akalla mutum 1, 037 sannan mutum 1,204 suka jikkata, galibinsu suna cikin mawuyacin hali.
Labari mai alaka: Mummunar girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 1000 a Morocco
Bayan jami’ai sun yi wa sarki bayani kan lamarin, ya bayar da umarni a yi gaggawar kafa "hukuma da za ta yi gaggawar sake gina wuraren da suka lalace tare da bayar da tallafi da kula da mutanen da ke cikin mawuyacin hali, musamman marayu da masu rauni".
Kazalika ya bayar da umarni a samar da "makwanci da abinci da dukkan abubuwan bukata" ga mutanen da ke bukata, da kuma bude wani asusu na musamman a babban bankin kasar domin tara taimako.
Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce girgizar kasar mai karfin maki 7.0 ta fi barna a larduna da biranen al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant.
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta yi gargadin cewa za a shafe shekaru kafin a gyara barnar da girgizar kasar ta yi.
An ji wasu kananan motsin kasa a biranen Rabat, Casablanca da Essaouira, yayin da aka ji karar girgizar kasar a Algeria da Mauritania.