Ghana ta zama kasa ta farko da ta amince ta yi amfani da wani sabon rigakafin zazzabin cizon sauro da ake gani zai kawo sauyi game da yadda ake rigakafin cutar.
Masana kimiyya na Jami'ar Oxford ne suka samar da rigakafin, mai suna R21 - wanda bincike ya nuna cewa yana aiki sosai idan aka kwatanta da wadanda aka samar a baya.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ghana ta amince a yi allurar rigakafin ga yaran da ke tsakanin wata biyar zuwa shekara uku.
Sauran kasashen Afirka ma suna nazari kan yiwuwar amincewa da allurar rigakafin.
A shekarar da ta gabata ne kamfanin Mosquirix, wani rukuni na kamfanonin hada magunguna na Birtaniya, GSK ya samar da rigakafin wanda Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta amince da shi.
Sai dai rashin isassun kudi ya sa kamfanin bai samar da isassun alluran rigakafi ba.
Zazzabin cizon sauro yana kashe kusan mutum 620,000 duk shekara, galibinsu kananan yara.
Gwajin da aka yi na rigakafin a Burkina Faso ya nuna cewa R21 yana aiki kusan kashi 80 idan aka yi wa mutum rigakafin sau uku, sannan aka kara yi masa daya sekara guda bayan na farko.