Ana sa rai matatar mai ta Dangote za ta riƙa aiki ɗari bisa ɗari a farkon shekarar 2025./Hoto:Dangote/X 

Ghana za ta iya fara sayen man fetur daga matatar Dangote da zarar ta fara aiki ɗari bisa ɗari, in ji shugaban ma’aikatar man fetur ta ƙasar, Mustapha Abdul-Hamid.

Abdul-Hamid ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa wannan matakin zai iya kawo ƙarshen maƙudan kuɗin da su kai dala miliyan 400 da ƙasar take kashewa wajen sayo mai daga Turai a ko wane wata.

"Idan matatar ta kai ga tace gangar mai 650,000 a ko wace rana, Nijeriya ba za ta iya shan dukkan man ba, saboda haka maimakon mu sayo fetur daga Rotterdam, zai fi sauƙi mu saya daga Nijeriya, kuma na yi imanin cewa wannan zai rage farashinsa a ƙasarmu," in ji Abdul-Hamid.

Ana sa rai matatar mai ta Dangote za ta riƙa aiki ɗari bisa ɗari a farkon shekarar 2025.

Abdul-Hamid ya ce sayen mai daga Nijeriya maimakon Turai zai sa farashin kayayyaki ya sauko a ƙasar ta Ghana tun da yin hakan zai ɗauke wa ƙasar kuɗin dakon man fetur daga Turai.

Ya ce daga baya ƙasashen Afirka za su cim ma yarjejeniya kan kuɗi na bai-ɗaya da za su riƙa amfani da shi, lamarin da zai rage tsadar dala.

Reuters