Ana kiwon kaji a Nijeriya saboda kasuwanci wasu kuma saboda sha'awa. Hoto/Others

Daga Abdulwasiu Hassan

Batun kiwon kaji a Nijeriya wanda ake yinsa domin kwai da nama na ci gaba da jan hankalin 'yan kasar musamman saboda kwastamomi suna kara nuna bukatarsu ta cin kajin gargajiya fiye da na Turawa ko broiler.

Kajin gargajiya ko kuma na gida sun fi tsada kuma ba su da saurin girma yayin da na gidan gona ko kuma broiler suna da saurin girma kuma sun fi nama amma duk da haka jama’a sun fi son na gargajiya.

Musa Isiyaku, wani mai sayar da kaji a kasuwar Dawanau da ke Kanon Nijeriya, ya ce samun kajin da za su wadaci kwastamominsu wani kalubale ne. “Akasarin kwastamomina sun fi son kajin gargajiya.

Masu kiwon kaji sun bayyana cewa an fi bukatar kudi wurin kiwon kajin Turawa fiye da na gargajiya. Hoto/Reuters

Idan ba a same su ba, sun gwammace kada su sayi komai,” kamar yadda Musa ya shaida wa TRT Afrika.

Ya ce bambanci tsakanin kazar gida da ta Turawa bai tsaya kan batun dandano da kudi ba, har ma kan dadewar naman.

“Idan aka soya kazar gargajiya, za ta iya yin mako guda ba ta lalace ba. Amma naman ta Turawa zai iya lalacewa kwana guda bayan dafawa,” in ji shi.

Neman kaji a kauyuka

Sana’ar sayar da kajin gargajiya sana’a ce mai kawo kudi.

Sana’ar ita ce wadda Musa da masu irin sana’ar a wani lokaci suke gwagwarmaya domin ganin sun samar da kajin ga kwastamominsu sakamakon karancin kajin.

Musa ya ce yana samun ribar kusan naira 80,000 a duk rana daga sayar da kajin gida.

A lokacin da ake samun kasuwar kajin matuka wanda shi ne lokacin girbe amfanin gona, ana iya yin cinikin sama da naira dubu 100 a duk rana, in ji shi.

Mutanen da ke kiwon kaji a gida akasari suna kai wa ‘yan kasuwa irinsa domin su kuma su sayar.

Haka kuma ‘yan kasuwa da dama irinsa na kai ziyara kauyuka domin neman kajin da suka girma domin kara sayar da su a kasuwar Dawanau da ke Kano.

Akasarin kajin gargajiya a Nijeriya ana kiwata su a kauyuka kafin a kai su kasuwa. Hoto/Reuters

Akwai wasu ‘yan sari da ke zuwa har Jamhuriyyar Nijar domin neman kaji, kamar yadda Musa ya bayyana.

“Wadannan akasari manyan ‘yan kasuwa ne wadanda suke sayar da kajin da suka kai kimanin naira 500,000 zuwa miliyan daya a rana,” in ji Musa.

Nama mai zaki

Akasari kiwon kaji domin kasuwanci a Nijeriya ana yinsa ko dai da kajin Turawa na boriler domin nama ko kuma masu kwai wadanda aka fi sani da layers ko kuma wadanda suke kwai kuma a samu nama daga gare su wato noiler.

Ana yawan sayen gasassun kaji a Nijeriya. Hoto/Reuters

Ba da dadewa ba, wasu manoma a arewacin Nijeriya sun kara inganta yadda suke kiwon kajin gargajiya bisa tsari domin biyan bukatar kwastamominsu.

Daya daga cikin masu bin wannan tsari shi ne Abba Hassan mazaunin garin Kano. Hassan na ganin za a fi samun riba idan aka mayar da hankali wurin kiwon kajin gida fiye da na Turawa, idan mai kiwon ya bi ka’idojin da suka dace.

“Duk mun san cewa kajin Turawa namansu ya fi zaki kuma ba su cika kamuwa da cuta ba, sai dai babbar matsalarsu ita ce rashin girma da wuri,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Aure tsakanin kajin Turawa da na gargajiya na bai wa mai kiwo damar samun kaji masu girma ba tare da an samu raguwa a kan ingancin nama ba da kuma juriya irin ta gargajiya ba.

Kyankyasar kaji

“Sakamakon auren na kajin, adadin kajin na gargajiya na karuwa daidai da kasuwa ba tare da sun rasa dandano ba sa’annan kuma su zama masu juriya ga cututtuka,” in ji Hassan.

Kajin Turawa ko kuma broiler sun fi saurin girma fiye da na gargajiya. Hoto/Reuters

Masu kiwon kaji na sayen ‘yan tsaki tun kafin a kyankyashe su inda ake biyan kudinsu kafin a samu.

“Amma idan kana son na gargajiya, sai dai ka siyar ita uwar kazar,” kamar yadda Hassan ya bayyana.

“A baya mutane na kiwon kajin gargajiya domin sha’awa ko kuma al’ada. Amma tuni duniya ta ci gaba. A halin yanzu, ina tunanin ta yadda zan yi kiwon kajin gargajiya a matsayin sana’a,” in ji shi.

Hassan na kallon auren kajin ba wai a matsayin hanyar sirkawa ba, amma a matsayin hanyar kara wa kajin inganci.

“Kajin gargajiya za su iya samar da karin ‘yan tsaki ta hanyar taimaka musu kyankyanshe kwayaye da injin kyankyasa na gargajiya. Kaji sun fi yin kwai idan aka dauke musu aikin kyankyashe kwai,” in ji shi.

TRT Afrika