Bassirou Diomaye Faye zai zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a Afirka. / Hoto: OTHER

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru a ranar Talata inda ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a ƙasar.

Faye ya lashe zaɓe ne kwanaki goma bayan ya fito daga kurkuku.

Ɗan kishin Afirka mai shekara 44, ba a ƙasar Senegal kaɗai zai zama shugaba mafi ƙarancin shekaru ba, har ma a dukkan Afirka.

Shugabannin Afirka da dama ciki har da na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, sun halarci bikin rantsar da shi a garin Diamniadio kusa da babban birnin Dakar.

Nan gaba kaɗan za a a yi bikin miƙa mulki a hukumance tare da Shugaba Macky Sall a fadar shugaban ƙasa da ke Dakar.

Faye na ɗaya daga cikin ƴan siyasar adawa da aka saka daga kurkuku kwanaki 10 kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a ranar 24 ga Maris. Ya fita daga gidan yari bayan afuwar da Shugaba Sall ya yi wa wasu fursunonin siyasa.

Tsohon jami'in hukumar karɓar haraji

An fara gangamin zaɓen Faye tun yana ɗaure a kurkuku.

Tsohon ma'aikacin hukumar tattara harajin zai zama shugaban ƙasar ta Yammacin Afirka na biyar tun bayan samun ƴancin kanta a 1960.

Faye da ya yi aiki tare da mai gidansa Ousmane Sonko, wanda aka haramta wa tsayawa takara. A yayin jawabin nasararsa ya bayyana abubuwan da za su bai wa muhimmanci: sulhu tsakanin ƴan ƙasa, sauƙaƙa tsadar rayuwa da yaƙi da cin-hanci.

Sabon zaɓaɓɓen shugaban na Senegal ya kuma yi alƙawarin dawo da ƙarfin ikon ƙasar, musamman a ɓangarorin man fetur, gas da kamun kifi.

Gyauron mulkin mallaka

Faye na son rabuwa da kuɗin CFA franc, wanda yake kallo a matsayin gyauron mulkin mallakar Faransa, a kuma zuba jari a ɓangaren noma da manufar samar da isasshen abinci a ƙasar.

Bayan shekara uku na rikici da hatsaniyar da aka rasa rayuka a ƙasar da aka sani da zaman lafiya, tun daga Washington zuwa Paris an taya murnar nasarar da ya samu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a ranar Litinin ya yi magana ta wayar tarho da zaɓaɓɓen shugaban inda ya bayyana shirin Amurka na ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.

Gwamnatocin soji

A matakin ƙasa da ƙasa, Faye na son dawo da ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soji, cikin ƙungiyar ECOWAS.

Faye da aka fi sani da Diomayem ko "Mutum Mai Daraja" a yaren Serer, ya lashe zaɓen da kaso 54.3 na ƙuri'un da aka jefa.

Abubuwa sun sauya bayan da gwamnati ta rushe jam'iyyar Pastef da ya kafa tare da Sonko a 2014, inda Sall kuma ya ɗage lokacin zaɓe.

Faye, matashin ɗan siyasa kuma cikakken Musulmi da ya fito daga gida mai ƙanƙan da kai, na da mata biyu da ƴaƴa huɗu.

Manyan ƙalubale

Sai dai kuma Faye da gwamnatin da zai kafa na da manyan ƙalubale da za su fuskanta.

Ba shi da rinjaye a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, a saboda haka sai ya yi ƙoƙarin ƙulla ƙawance don yin dokoki, ko ya yi kira da a sake gudanar da sabon zaɓen ƴan majalisar a tsakiyar watan Nuwamba.

Babban ƙalubalen da ke gabansa shi ne samar da ayyukan yi ga ƴan ƙasar da kaso 75 na jama'arta su miliyan 18 ƴan ƙasa da shekara 35 ne, kuma alƙaluman rashin aikin yi ya kai kashi 20 cikin ɗari.

Matasan ƙasar da dama sun fitar da rai ga makomarsu a ƙasar inda suke jefa rayuwarsu cikin hatsarin bin hanyar teku don shiga Turai.

TRT Afrika