Wannan nadi ya zo ne kwana daya bayan da majalisar Ethiopia ta cire jam’iyyar ‘yan tawayen Tigray daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda/Photo Reuters

Firaministan Ethiopia, Abiy Ahmed ya nada Getachew Reda, wani babban jami’in kungiyar tawaye ta Tigray People's Liberation Front (TPLF), a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya ta yankin Tigray.

Matakin wani bangare ne na aiwatar da yanjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a shekarar da ta gabata, tsakanin gwamnatin tarayyar Ethiopia da kuma TPLF.

Wannan yanjejeniya ce ta kawo karshen kazamin rikicin da ya dauki shekaru biyu, wanda kuma ya janyo salwantar rayukan dubban mutane, da tagayyara miliyoyi.

Wannan nadi ya zo ne kwana daya bayan da majalisar Ethiopia ta cire jam’iyyar ‘yan tawayen Tigray daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Wannan wani karin gagarumin mataki ne na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Majalisar kasar ta amince da kudurin kafa gwamnatin rikon-kwarya ta yankin Tigray, wadda a yanzu Getachew Read zai jagoranta.

Sabon shugaban rikon kwaryan na Tigray, zai dauki gabarar jagorantar hukumar zartarwar yankin.

Wannan zai mai da hankali kan kafa gwamnati mai wakilancin domin tabbatar da wakilcin kungiyoyin siyasa masu yawa da ke da tasiri a yankin.

Yakin da aka gwabza tsakanin sojojin gwamnatida na ‘yan tawayen Tigrayya fara ne a shekarar 2020.

Yakin ya lafa bayan da bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Afirka ta Kudu, da kuma a Kenya cikin Nuwamban da ya gabata.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na shekarar da ta gabata, ya ayyana adadin mutanen da suka tagayyara sakamakon yakin kan kimanin miliyan 2.7. Sannan yara miliyan 12.5 sun shiga matsananciyar bukata jin-kai.

TRT Afrika