Ƙasashen Yammacin Afirka a ranar Lahadi sun bai wa ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji wata shida su sake nazari kafin ficewarsu daga ƙungiyar ECOWAS.
Wannan matakin na ECOWAS na zuwa ne bayan ƙasashen uku waɗanda suka kafa ƙungiyar Sahel Alliance sun jaddada cewa "ba za su koma ƙungiyar ta ECOWAS ba", amma za su amince a riƙa shige da fice a tsakanin ƙasashen ba tare da biza ba.
Ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da zama ‘yar ‘amshin-shata ga Faransa, wadda ita ce ta yi musu mulkin mallaka, amma a yanzu suka raba gari da ita.
Ficewar ƙasashen uku daga ECOWAS zai yi tasiri matuƙa kan kasuwanci da kuma zirga-zirgar jama'a da jigilar kayayyaki da kuma tsaro a yankin wanda ke fama da ta'addanci.
A ƙarƙashin dokar ECOWAS, ya kamata ficewarsu daga ƙungiyar ta zama ta fara aiki ne a watan Janairu mai zuwa, shekara guda bayan ƙasashen suka yi sanarwarsu ta farko ta ficewa daga ƙungiyar.
Sai dai bayan tattaunawar da aka gudanar da ƙungiyar ta gudanar a Abuja, ƙungiyar a cikin sanarwar da ta fitar ta ce ta saka tsakanin 29 ga Janairun 2025 zuwa 29 ga Yulin 2025 a matsayin wani wa'adi domin barin ƙofar ƙungiyar a buɗe ga ƙasashen uku ko da kuwa za su sake nazari kan ficewar tasu.
Haka kuma ƙungiyar ta ECOWAS a zaman da ta yi a ranar Lahadi 15 ga Disamba ta amince a kafa wata kotu ta musamman domin yin hukunci dangane da laifukan da aka aikata a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Gambia Yahya Jammeh.
Ƙasashen na Mali da Burkina Faso da Nijar ba su tura ko da wakili ɗaya a yayin taron da aka gudanar a Abuja ba.
Sai dai a ranar Juma’a shugabannin ƙashen uku sun yi taron nasu a Yamai babban birnin Nijar inda a nan ne ma suka jaddada cewa “ba za su koma ƙungiyar ECOWAS ba”.
Bayan kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun bayyana matakin ficewa daga kungiyar, ECOWAS ta nada shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin mai shiga tsakani da zai jagoranci tattaunawa da kasashen uku da suka kafa Sahel Alliance.
An kuma zabi shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe domin shiga tattaunawar a madadin kungiyar ECOWAS.
A halin yanzu waɗannan shugabannin biyu za su ci gaba da tattaunawa da ƙasashen domin ƙoƙarin shawo kan ƙasashen da kuma lalubo mafita.
Duk da cewa har yanzu ECOWAS ɗin ba ta yi nasara a ƙoƙarin da take yi na lallashin ƙasashen uku su yi haƙuri ba, amma Faye ya ce “akwai ci gaba” a halin yanzu.