Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Mogadishu, babban birnin Somalia domin nuna adawa da yarjejeniyar da kulla tsakanin Ethiopia da yankin Somalilanda da ya balle daga Somalia wadda ta ba da dama a yi amfani da ruwan yankinsu.
Masu zanga-zangar sun taru a Filin Easa na Injiniya Yariisow da ke Mogadishu bayan sun karade tituna daban-daban.
Wasu daga cikin jami'an gwamnati ciki har da Ministan Cikin Gida Ahmed Moalim Fiqi, mambobin majalisun dokokin Somalia da Magajin Birnin Mogadishu Yusuf Hussein Jimaale sun halarci zanga-zanga inda suka yi tir da yarjejeniyar.
Masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye da aka rubuta “Somali ta 'yan Somalia ce” da “tekunmu ba na sayarwa ba ne.”
Tashar ruwa a Bahar Maliya
An rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugaban kasar Somaliland, Muse Bihi Abdi a babban birnin Habasha, Addis Ababa ranar Litinin, wanda zai ba wa Habasha dama kan tashar ruwa ta Bahar Maliya.
Ofishin Firaminista Abiy ya yaba wa yarjejniyar a matsayin "mai cike da tarihi", inda ya ce "manufar ita ce samar da bigiren na gina hadin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin bangarorin biyu."
Kungiyar yankin gabashin Afirka IGAD ta bayyana "matukar damuwa" game da da jijiyar wuya tsakanin Habasha da Somalia, kuma ta yi gargadi kan yuwuwar samuwar matsalolin dorewar zaman lafiyar yankin.
Kungiyar ta yi kira ga kasashen biyu d asu "hada kai don cimma warware matsalar cikin lumana", kamar yadda wata sanarwa daga Babban Sakataren, Workneh Gebeyehu.
Kare 'yancin cin gashin kai
Yayin da yake magana da masu zanga-zanga, Fiqi ya sha alwashin cewa Somaliya za ta kare 'yancinta da iyakokinta, kuma ya zargo Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shiga rikicin yankin da assasa rabuwar kai.
Fiqi ya kara da cewa "Ganin yadda ya sanya hannu kan yarjejeniya kuma ya ce zai amince da 'yancin-kan Somaliland a matsayin kasa mai' yanci, tamkar yana cewa ne babu kasar Somaliya, kuma ba za mu amince da wannan ba."
A ranar Talata, Somaliya ta yi watsi da shirin na tashar ruwan Bahar Maliya da kasar Somaliland, inda ya kira shirin a matsayin barazana ga kyakkyawar makotaka da keta haddin 'yancin kanta.
Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheik Mohamud a daren Talata ya kira takwaransa na Masar bayan faruwar tashin tashina tsakanin Somaliya da Habasha game da shirin.
Goyon baya daga Masar
Shugaban Masar ya jaddada wa tskawaransa na Somaliya, cewa Masar za ta goyi bayan Somaliya, kuma ta ba ta tallafi kan tsaro da dorewar zaman lafiya.
Haka kuma, Somaliya ta yi kiranye ga jakadanta na Habasha, bayan da majalisar mulkinn Somaliya ta gudanar da wani taron gaggawa a babban birnin kasar, wanda Firaminista Hamza Abdi Barre ya jagoranta.
Somaliland wani yanki ne da ya kasance karkashin mulkin Burtaniya, kuma yana arewa maso yammacin Somaliya. Yankin ya yi shelar 'yancin-kai a shekarar 1991, amma bai samu amincewa daga kasasehn duniya ba.
Habasha ta rasa tashoshinta na Bahar Maliya a farkon shekarun 1990, bayan da yakin neman 'yanci na Eritrea, wanda ya dauki tsawon lokaci daga 1961 zuwa 1991.
Rasa gabar teku
A shekarar 1991, Eritrea ta samu 'yancin kai daga Habasha, wanda ya janyo kafuwar kasashe biyu a rarrabe. Rabuwar ta haifar da Habasha ta rasa damar kai-tsaye da Tekun Maliya da gabobin ruwa.
Tun lokacin ne Habasha ta zamo mara iyakar ruwa, wanda ya yi tasiri kan karfinta na kasuwanci ta hanyoyin ruwa.
Habasha da Masar sun shiga takun-saka tsawon shekaru sakamakon shirin gina madatsar ruwa a Kogin Nilu, wanda Habasha take yi.
A watan jiya, Masar ta sanar da rashin samun daidaito a tattaunawarsu da Habasha da Sudan game da gina madatsar ruwan ta Renaissance Dam, kuma ta sha alwashin kare ruwan kasarta, da kuma tsaron kasarta matukar aka mata barazana.