Mutane da dama sun ta yada wannan bidiyo a shafukan sada zumunta. Photo/SP Gambo

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Katsina da ke arewacin kasar ta karyata wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda aka yi ikirarin cewa an ga saukar wata bakuwar halitta a jihar.

A cikin bidiyon, an ga wani abu kamar kwarangwal yana tafiya sai kuma wani mutum yana salati yana cewa “yanzun nan muka ga saukar wani jinsin Alien (bakuwar halitta) da ya taho daga duniyar Mars ya fado a nan cikin Jihar Katsina”.

Mutumin ya yi ikirarin cewa lamarin ya faru ne daga ketaren titin Ring Road hanyar da za ta kai mutum Unguwar Dutsen Safe.

Sa’annan an ga halittar na kuka irin na kura inda mutumin ya ce halittar ta gansu kuma za ta biyo su.

Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Katsina SP Gambo Isah ya fitar ranar Litinin ya ce, “bidiyon gaba dayansa karya ne kuma wasu masu mugun nufi ne da ke yunkurin kawo cikas a zaman lafiyar da mutanen jihar ke ciki suka shirya shi.

“Saboda haka, ana bukatar jama’a baki daya da kada su tsorata kuma su yi watsi da wannan bidiyon na bogi da kuma abin da ke cikinsa,” in ji sanarwar.

Mutane da dama dai sun ta yada wannan bidiyo a karon farko a shafukan sada zumunta da kuma dandali daban-daban na Whatsapp inda suke neman karin bayani kan sahihancinsa.

Jihar Katsina na fama da matsalolin hare-haren 'yan bindiga lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

TRT Afrika