Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaron kasar da babban sifeton 'yan sanda da kuma shugaban hukumar kwastam.
Wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan watsa labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayyar kasar ya fitar ranar Litinin, ta ce shugaban kasar ya kuma nada sabbin manyan hafsoshin tsaron.
Mutanen da shugaban ya nada su ne:
1. Mallam Nuhu Ribadu - Mai bayar da shawara kan Sha'anin Tsaro
2. Manjo. Janar C.G Musa - Babban Hafsan Tsaro
3. Manjo. T. A Lagbaja - Babban Hafsan Sojin Kasa
4. Rear Admirral E. A Ogalla - Babban Hafsan Sojin Ruwa
5. AVM H.B Abubakar - Babban Hafsan Sojin Sama
6. DIG Kayode Egbetokun - Babban Sifeton 'yan sanda na rikon kwarya
7. Manjo Janar EPA Undiandeye - Shugaban Hukumar Leken Asiri
8. Adeniyi Bashir Adewale - Shugaban rikon kwarya na Hukumar Kwastam
Kazalika shugaban kasar ya nada:
1. Kanar Adebisi Onasanya - Kwamandan Brigade of Guards
2. Laftanar Kanar Moshood Abiodun Yusuf - Kwamandan Bataliya ta 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja
3. Laftanar Kanar Auwalu Baba Inuwa - Kwamandan 177, Bataliya ta Guards Battalion, Keffi, jihar Nasarawa
4. Laftanar Kanar Mohammed J. Abdulkarim - Kwamandan Bataliya ta 102 Guards Battalion, Suleja, Neja
5. Laftanar Kanar Olumide A. Akingbesote - Kwamandan Bataliyar 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Tinubu ya nada:
-Hadiza Bala Usman a matsayin Mai ba shi shawara ta musamman kan Tsare-Tsaren Ayyuka
- Hannatu Musa Musawa – Mai ba shi shawara kan Tattalin arzikin Al’adu da Nishadantarwa
- Sanata Abdullahi Abubakar Gumel – Babban mai ba shi shawara kan Majalisar Dattawan Nijeriya
-Honorabul (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim – Babban mai ba shi shawara kan Majalisar Wakilai