Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta aike da gaisuwar ta'aziyyarta ga iyalan mutanen da gobarar ta yi sanadiyar mutuwarsu.Hoto \ Reuters

Canada ta dakatar da ayyuka a ofishin jakadancinta da ke Nijeriya har sai yadda hali ya yi, kana ta yi gargadi ga 'ya'yanta kan yawan tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa kasashen yammacin Afirka.

Tuni aka kaddamar da bincike bayan tashin gobarar a ofishin jakadancin a ranar Litinin wadda ta yi sanadin mutuwar mutum biyu, a cewar Ministar harkokin wajen kasar Melanie Joly.

Jami’an kashe gobara sun ce wani tankin ajiye fetur da ke cikin ginin injin janereto ne ya kama da wuta, inda ma'aikata biyu da ke kula da janaretan suka mutu.

Kazalika mutane biyu sun jikkata sakamakon tashin gobarar.

"Muna tabbatar da cewa an samu fashewar wani abu a babban Ofishin jakadancinmu a Nijeriya, gobara ce ta tashi kuma muna bincike don gano musabbabin abin da ya faru," in ji Joly a shafinta na X.

Sai dai babban Ofishin bai ce komai ba game da gobarar amma a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce an "dakatar da ayyukan Ofishin har sai baba ta gani."

Mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Ajuri Ngelale, ya ce an samu asarar rai da wadanda suka jikkata a gobarar amma bai bayyana adadin mutanen ba, a cewar wata sanarwa da ya fitar.

Sharudda kan tafiye-tafiye

Ofishin jakadancin ya fitar da wasu sharudda kan tafiye-tafiye, inda ya bukaci 'yan kasar Canada su guji yin balaguro mara muhimmanci zuwa Najeriya, ciki har da Abuja babban birnin kasar, "saboda yanayin tsaro na rashin tabbas a duk fadin kasar da kuma hadarin hare-haren ta'addanci da laifuka da rikice-rikicen kabilanci da kuma hare-hare da makamai da garkuwa da mutane."

A ranar Juma'a ne kasar Amurka da Birtaniya suka fitar da sanarwar cewa akwai "mummunar barazana ga manyan otal-otal a manyan biranen Nijeriya" tare da gargadi kan tafiye-tafiye zuwa kasar mafi yawan al'umma a Afirka.

Kasashen Yamma da ke da ofisoshin jakadanci a Nijeriya suna yawan fitar da sanarwar gargadi kan tafiye-tafiye zuwa kasar, lamarin da gwamnati Nijeriya ta sha watsi da sha yin watsi da shi.

TRT Afrika