Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi haɗin kan gwamnonin ƙasar 36 wajen gaggauta shawo kan hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
A taron da ya yi da gwamnonin a ranar Alhamis a fadarsa da ke Abuja, Shugaba Tinubu ya ce babu wani da ya fi muhimmanci a gare shi a yanzu da ya wuce samar da abinci ga al'ummar ƙasar.
“Ba wani abu da muke yi da ya fi samar da abinci mai inganci don mutanenmu su ci, su saya, su sayar. Muna samar da ayyukan yi a yayin samar da shi (abincin). Kuma wannan shi ne kafin mu samar da arziki ta hanyar fitar da abin da ya wuce ƙima. Babu abin da ya wuce mu cimma wannan buri don ‘yan Nijeriya," ya faɗa.
Shugaba Tinubu ya kuma bukaci gwamnonin jihohin da su hada kai don biyan bukatun ‘yan kasa, inda ya bayyana cewa a shirye yake ya ba da tallafin da ake bukata domin ganin ‘yan Nijeriya sun samu sauki daga halin ƙunci.
"Wane irin tallafi kuke buƙata daga gare ni kuma ta wace hanya? Ni a shirye nake na bayar da shi. Amma dole ne mu cimma sakamakon. Dole ne mu kai ga cimma burinmu a kowane mataki. Da fatan za ku ba da rahoto kan shawarwarin da kuka yanke kuma ku miƙa wa ofishina a cikin kwana bakwai,” in ji Shugaba Tinubu.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci da ma ƙarancinsa a Nijeriya, lamarin da ke tayar da hankulan al'ummar ƙasar.
Sauran muhimman abubuwan da Shugaban Ƙasar ya amince da su a yayin ganawarsa da gwamnonin sun haɗa da:
1. Bai wa iyalai 100,000 a kowace jiha tallafin N50,000 har tsawon wata uku.
2. Ware Naira biliyan 155 domin sayen kayan abincin da za a tallafawa masu ƙaramin ƙarfi kan farashi mai rahusa.
3. Bai wa kowace jiha Naira biliyan 10 domin sayen motocin sufuri masu aiki da iska gas domin sauko da farashin kuɗin zirga-zirga.
4. Gaggauta fara aikin hanyar da ta tashi daga Sokoto zuwa Badagary a Lagos, wacce za ta ratsa ƙauyuka kimanin 216 da madatsun ruwa (dams) guda 58 da ƙananan hukumomi 156 da manyan garuruwa 39 da kuma gonaki da suka kai kimanin eka miliyan ɗaya. Titin zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Lagos.
5. Shugaba Tinubu ya kuma amince da biyan kuɗin aikin hanyar jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri wadda za ta ratsa jihohin Rivers da Abia da Enugu da Binuwai da Nasarawa da Filato da Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Borno.
6. Haka nan an amince da biyan kuɗin da ake buƙata domin yin aikin hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Ibadan zuwa Abuja a wani ɓangare na aikin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Aikin zai haɗa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Neja da Abuja da Kaduna da kuma Kano.
7. Shugaban Ƙasa ya kuma ba da umarnin ci gaba da aikin hanyar Lagos zuwa Calabar wadda kuma za ta yi rassa a jihohin Binuwai da Kogi da Nasarawa da Enugu da Ebonyi da kuma babban birnin ƙasar Abuja.