Hukumar jinƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya tana fuskantar ƙalubale na tattara kuɗi domin bayar da tallafin abinci ga yankin arewa maso gabashin Nijeriya wanda ke fama da rashin abinci da rashin tsaro, abin da ya haifar da fargaba kan yiwuwar faɗawa cikin bala'in yunwa da mace-mace, kamar yadda babban jami'in hukumar ya yi gargaɗi.
A watan Afrilu, Ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya(OCHA) ya ƙaddamar da wani shiri na dala miliyan 306 tare da tallafin Nijeriya domin samar da abinci ga mutane miliyan 2.8 a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, yankin da ya daɗe yana fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Babban jami'in OCHA Mohamed Malick Fall ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, duk da yake da farko gwamnatin Nijeriya ta bayar da dala miliya 11 inda ita ma MDD ta bayar da nata dala 11, har yanzu ba a cim ma gaci ba saboda sauran masu bayar da tallafi na duniya sun ƙi bayar da nasu kason.
"Akwai gagarumin aiki a gabanmu. Wannan shi ne halin da muke ciki a yayin da muke cikin damuna, mun lura cewa tallafin da ake bai wa Nijeriya yana ci gaba da raguwa," in ji Fall a tattaunawar da ya yi ranar Alhamis.
Fall ya yi hasashen cewa da wahala su samu abin da ya kai dala miliyan 300, abin da ke nufin an samun raguwa daga dala miliyan 500 da suka samu a bara. Ya ɗora alhakin wannan raguwa kan tasirin da annobar korona ta yi ga ayyukan ƙungiyoyin da ke bayar da tallafi na duniya.
Rikice-rikicen da ke faruwa a sassan duniya sun kawar da hankulan ƙungiyoyin bayar da agaji daga Nijeriya, in ji shi.
"Gaza, Ukraine, da Sudan sun faɗa cikin rikici a shekaru biyu da suka gabata abin da ya sa yake da matuƙar wahala a ci gaba da bayar da tallafi kamar yadda yake a baya," a cewar Fall.
Ya ƙara da cewa matsalar ta ta'azzara ne sakamakon tsadar rayuwar da ta yi ƙamari a Nijeriya, inda hauhawar farashi ya zarta kaso 33 cikin ɗari sannan farashin kayan abinci ya tashi fiye da kashi 40.
OCHA ta yi gargaɗi cewa za a fuskanci "babban bala'i" sakamakon rashi abinci a arewa maso gabashin Nijeriya muddin ba a kai ɗaukin gaggawa ba.
Wasu alƙaluma da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya fitar a watan Afrilu sun nuna cewa yara fiye da 120,000 a yankin aka kai asibiti sakamakon kamuwa da tamowa, idan aka kwatanta da yara 90,000 da aka yi hasashe za su fuskanci matsalar.
"Rashin ɗaukar mataki zai haifar da matsaloli da dama waɗanda suka haɗa da mutuwar yara," in ji Fall.