Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS tana buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don samar da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro da za ta yi yaƙi da ta’addanci, a cewar ɗaya daga cikin zaɓuka biyun da hukumomin tsaro na ƙasashen yankin ke duba yiwuwarsu a taron da suka yi a yau Alhamis.
Ministocin Tsaro da na Kuɗi na Ƙasashen ECOWAS sun yi taron a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da kuma yawan kuɗaɗen da ake buƙata don samar da ita.
Afirka ta Yamma na fama da matsalolin juyin mulki, lamarin da yake zama matsala ga tsarin siyasa da jawo rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen yankin.
A watan Janairu, shugabannin mulkin soji na Nijar da Burkina Faso da Mali sun yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar mai mambobin ƙasashe 15.
Ministan Tsaron Nijeriya ya shaida wa taron cewa akwai zaɓi biyu a samar da rundunar yankin: Daya za a kashe dala biliyan 2.6 duk shekara a kan runduna mai dakaru 5,000, dayan kuma za a kashe dala miliyan 481 a dakaru 1,500
“Wadannan alkaluma sun nuna muhimmancin aikin da ke gabanmu,” in ji Badaru. "Don haka ya zama wajibi mu yi nazari sosai kan zabin duba da irin kalubalen da yankinmu ke fuskanta a halin yanzu da kuma matsalolin kudi da kasashe mambobinmu ke fuskanta."
Tun a shekarar 2020, sojoji a kasashen uku suka yi juyin mulki suna zargin shugabannin farar hula da ƙyale masu da'awar jihadi su samu galaba.
Da hawansu kan mulki, sojojin sun yi watsi da yarjejeniyoyin tsaro da aka ƙulla da sojojin Amurka da Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya tare da gayyatar Rasha da su maye gurbinsu.
Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ɗaukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai yaƙi da ta'addanci. Ana sa ran kowace ƙasa mamba za ta ba da gudunmawar wani kaso, in ji shi.
Shugaban hukumar ECOWAS Omar Touray ya ce ba za a cire mambobin da aka dakatar daga cikin rundunar yankin ba.
"An yi imanin ba za mu iya yaki da ta'addanci mu kadai idan har wasu ba su shiga ba," in ji Touray.
"Ko da yake ana iya dakatar da wasu kasashe amma ya kamata a bar su su shiga tarukan da suka shafi tsaro, shi ya sa muka gayyaci dukkan kasashe mambobi 15 da su halarci wannan muhimmin taro."