Keftin Ibrahim Traore ya zama shugaban ƙasa bayan juyin mulkin da ya yi a 2022. / Hoto: Others

Burkina Faso ta dakatar da kafafen watsa labarai da dama na Ƙasashen Yamma, waɗansu daga cikinsu dakatarwa har ta sai baba ta gani.

Daga cikin waɗanda aka dakatar akwai jaridar Faransa ta Le Monde da The Guardian ta Birtaniya da Deutsche Welle ta Jamus da TV5 Monde ta Faransa, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta CSC ta sanar.

An dakatar da su ne sakamakon wani rahoto da suka bayar na ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch HRW wadda ya zargi sojojin da kai hari kan fararen hula a yaƙin da sojojin ke yi da masu tayar da ƙayar baya.

Sauran kafafen watsa labaran da aka dakatar a sanarwar ta baya-bayan nan sun haɗa da jaridar Ouest-France da APAnews da Agence Ecofin.

‘Zargi maras tushe’

Tun a ranar Alhamis, hukumar ta CSC ta bayar da umarni ga kamfanonin da ke samar da intanet kan su dakatar da shafukan BBC da VOA da Human Rights Watch daga Burkina Faso na tsawon makonni biyu.

Sojojin da ke mulki a Burkina Faso sun yi watsi da “zargi maras tushe” waɗanda ƙungiyar HRW ta yi na cewa sojojin sun kashe mutum aƙalla 223 a wani ƙauye yayin wani samame da suka kai a ranar 25 ga watan Fabrairu.

“Kisan da aka yi a Nodin da Soro sun sa an soma bin matakan shari’a,” kamar yadda ministan watsa labarai Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ƙungiyar HRW ta bayyana kisan kiyashin a matsayin ɗaya daga cikin “take haƙƙin bil’adama mafi muni da sojoji suka yi a Burkina Faso tun daga 2015”.

“Irin waɗannan kashe-kashen na daga cikin hare-haren da sojojin ke kaiwa kan farar hula waɗanda ake zarginsu da haɗa kai da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai, wanda hakan zai iya jawo aikata laifi ga bil’adama,” kamar yadda ƙungiyar ta Humar Rights Watch da ke New York ta bayyana.

Ƙasar da ke Yammacin Afirka wadda ke ƙarƙshin mulkin soja tun daga 2022, ta sha fama da matsalolin ta’addanci waɗanda suka faro tun daga Yammacin Mali a 2015.

AFP