Wata mata a Niejriya ta shaida wa Reuters rundunar sojin ƙasar ta zaubar mata da ciki a ɓoye, sai da rundunar ta ƙaryata wannan zargi./ REUTERS

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Nijeriya ranar Juma'a ta ce binciken da ta gudanar "bai gano wasu shaidu" cewa rudunar sojin ƙasar da gangan ta kai hare-hare kan mata da ƙananan yara ko kuma zubar da cikin mata a ɓoye ba a yaƙin take yi a arewa maso gabashin ƙasar.

Hukumar, wadda gwamnati ta kafa, ta gudanar da bincike kan wani labari na kamfanin dillancin labarai na Reuters na watan Disambar 2022 wanda ya yi zargin cewa rundunar sojojin Nijeriya tana zubar da cikin matan da aka kama da zargin kasancewa mambobin ƙungiyar Boko Haram tare da kashe ƙananan yara, a yaƙin da ta shafe fiye da shekaru 15 tana yi da ƙungiyar.

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Nijeriya ta fitar da wani rahoto bayan ta kwashe fiye da watanni 18 tana gudanar da bincike tare da tattaunawa da shaidu aƙalla 199, ciki har da sojoji da tsoffin 'yan Boko Haram da matan da aka fitar daga kurkuku bayan an zarge su da zama 'yan ƙungiyar da mazauna yankunan da ke fama da hare-haren ƙungiyar da ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashen waje da ke aiki a yankunan. Ba dukkansu rahoton ya ambata ba.

Cikin waɗanda aka tuntuɓa yayin gudanar da binciken har da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya Chris Musa, wanda a lokacin da aka yi zargin shi ne kwamandan da ke jagorantar yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a arewa maso gabas, da wanda ya gabace shi a kan muƙamin, Janar Lucky Irabor da tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya Laftanar Janar Farouk Yahaya.

Kwamitin mai mutum bakwai da ya gudanar da binciken, ya haɗa da manjo janar Letam Wiwa (mai ritaya) wanda ya taɓa aiki a matsayin shugaban sashen leƙen asirin rundunar sojin Nijeriya.

"Babu wata shaida da ta nuna cewa rundunar sojin Nijeriya ta zubar da cikin dubban mata da 'yan mata a ɓoye waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu tayar da ƙayar baya a arewa maso gabashin ƙasar," in ji rahoton, wanda aka fitar a wani taron manema labarai a Abuja.

A baya rundunar sojojin Nijeriya ta ƙaryata labarin na Reuters. Mai magana da yawun rundunar Edward Buba bai amsa buƙatar da aka tura masa ta yin tsokaci game da rahoton ba ranar Juma'a. Shi ma babban hafsan tsaron Nijeriya, Chris Musa, bai yi magana ba game da yunƙurin da Reuters ya yi na jin ta bakinsa game da batun ta wayar tarho ranar Juma'a.

Da yake magana game da binciken, mai magana da yawun Reuters ya ce: "Muna kan bakanmu game da labarin da muka bayar, wanda ya yi daidai da ƙa'idojin aikinmu a Reuters ba tare da nuna son-kai ba, kuma cikin sahihanci."

Sakamakon binciken

Binciken hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Nijeriya ya gano cewa rajistar asibitoci biyar na fararen-hula a arewa maso gabashin ƙasar ta nuna cewa an zubar da bai wuce 6,000 ba, daga 2013 zuwa 2022 amma ya ce babu wasu shaidu da suka nuna cewa an tilasta wa waɗanda suka zubar da cikin ko kuma an zubar da ciki ba bisa ƙa'ida ba a asibitocin soji da ma na fararen-hula.

Ya ƙara da cewa samun bayanai kan harkokin soji, da suka haɗa da bayanai na canjin wurin aki da kuma harkokin lafiyarsu, na cike da ƙalubale.

"Ba mu iya samun bayanai daga rundunar soji ba. Mun yi bakin ƙoƙarinmu amma mun gano cewa ba a ajiye bayanai kamar yadda ya kamata a kusan ɗaukacin asibitocin soji da muka ziyarta," a cewar lauyan kwamitin, Hilary Ogbonna.

Kwamitin ya ce bai samu wasu shaidu da ke nuna cewa sojoji sun ci mutuncin ƙananan yara da gangan ba, amma ya gano shaidu da ke nuna cewa sojojin Nijeriya sun kai hari a ƙauyen Abisari ranar 18, ga watan Yunin 2016, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 18, da suka haɗa da mata da yara.

Reuters