Wata mai zane-zane ƴar Faransa Prune Nourry da Jami'ar Obafemi Awolowo ne suka shirya fim ɗin mai taken: “Statues Also Breathe,” a Turancin Ingilishi. / Hoto: Reuters

An tantance wani fim a birnin Lagos na Nijeriya wanda za a nuna shi a wani ɓangare na cika shekaru goma da sace ƴan matan makarantar Chibok fiye da 200 da mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da su a shekarar 2014 a jihar Borno.

Wata mai zane-zane ƴar Faransa Prune Nourry da Jami'ar Obafemi Awolowo ne suka shirya fim ɗin mai taken: “Statues Also Breathe,” a Turancin Ingilishi.

Harin da mayakan Boko Haram suka kai makarantar mata ta Chibok inda suka kwashe ɗalibai fiye da 200 shi ne karo na farko da aka fuskanci babbar matsalar garkuwa da mutane a Nijeriya.

Tun daga wancan lokacin, an sace ɗalibai sama da 1,400 musamman a arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Ana sakin galibin waɗanda aka yi garkuwa da su bayan an bayar da kuɗin-fansa, ko da yake a wasu lokutan ƴan bindigar kan kashe su ko da an ba su abin da suka nema. Kazalika ba kasafai ake kama ɓarayin mutane ba.

Ƙalubalen da mata ke fuskanta wajen neman ilimi

“Mun yi wannan haɗin-gwiwa ne domin mu wayar da kan jama'a game da ƙalubalen da mata suke fuskanta a wajen neman ilimi,” in ji Nourry.

Fim ɗin na minti 17 ya nuna mutum-mutumai 108 — da ke alamta yawan ƴan matan da har yanzu ba a gan su ba — ya yi ƙoƙarin nuna yadda ƴan matan suka sauya daga wancan lokaci zuwa yanzu ta hanyar amfani da hotunansu da aka samu daga wurin danginsu.

Kazalika fim ɗin ya nuna wasu zane-zane na ƴan matan, waɗanda aka yi baje-kolinsu a watan Nuwamba na 2022, inda aka sassaƙa mutum-mutuman kawunansu ta hanyar bin tsarin yadda ake sassaƙa a masarautar Ife a Nijeriya.

Masu sharhi na ci gaba da nuna damuwa cewa tsaro na ƙara taɓarɓarewa tun bayan sace matan Chibok inda a yanzu makarantu da dama a yankin ke fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane.

AP