Birtaniya ta yi hayar jirgin ruwan da zai kwashi masu neman mafaka 500. Hoto: AFP  

Birtaniya na shirin mayar da baƙin haure kusan 6,000 zuwa kasar Rwanda a wannan shekarar, a cewar wani babban ministan kasar a ranar Talata, hakan ya biyo wasu bayanai da gwamnatin kasar ta fitar kan shirin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Alkaluman sun biyo bayan wasu kwanaki da shirin hana baƙin haure dake zuwa ta kananan kwale-kwale arewacin Turai ya zama doka bayan watannin da aka kwashe ana takaddama a majalisar kasar.

Rwanda dai 'ta amince' da karbar bakin haure 5,700 waɗanda suke Birtaniya a halin yanzu, kamar yadda ma'aikatar cikin gidan kasar ta bayyana a yammacin ranar Litinin.

Daga cikin mutanen ''za a iya tattara tare da tsare mutum'' 2,143 daga cikinsu kafin a tafi da su, a cewar ma'aikatar.

Hukumomin tsaro za su nemo sauran, a cewar Sakatariyar Lafiya ta kasar Victoria Atkins a ranar Talata a yayin da take amsa tambayoyi kan bakin-haure 5,700 da za mayar da su Rwanda.

"Abin da muke sa rai shi ne, mu fitar da rukunin mutanen ... a karshen shekara," kamar yadda ta shaida wa gidan talabijin na Sky News.

Sama da mutum 5,700 ne suka isa ta kananan kwale-kwale bayan da suka yi kokarin shiga wasu kasashe a cikin watanni 18, kamar yadda alkaluman hukumar suka nuna.

Tsayayyiyar ƙasa

Alkaluman sun bayyana irin girma matsalar da ake fuskanta a kokarin dakile kwararar bakin haure waɗanda ke zuwa ba bisa ka'ida ba, tare da takaita shirin gwamnati kasar na tura wasu daga cikinsu zuwa Rwanda.

A karkashin shirin -- wanda za a ware miliyoyin kuɗaden Fam na masu biyan haraji a Birtaniya- Kilgali ce za ta tattace matsayar samun mafakar da za su samu.

Idan aka amince, za a bar su su zauna a Rwanda kuma ba za su koma Birtaniya ba.

Kasar Rwanda mai dauke da mutane miliyan13 a yankin manyan tafkunan Afirka, ta yi ikirarin cewa ita ce daya daga cikin kasashen da suka fi kwanciyar hankali a nahiyar, kuma ta samu yabo ga ababen more rayuwa na zamani da ta ke da shi a kasar.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin ɗan adam na zargin ɗaddaden shugaban kasar Paul Kagame da gudanar da mulki cikin yanayi na tsoro da dakile ancin ƴan adawa da fadin albarkacin baki da kuma zargin da shugaban ya musanta.

Kalubale ga tsarin

A makon da ya gabata ne ƴan majalisar dokokin Birtaniya suka amince da dokar kare hakkoki ta Rwanda, wanda ya tilastawa alkalan Birtaniya aiyana kasar a matsayin kasa ta uku mafi aminci da tsaro.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun kolin Birtaniya ta yanke a bara kan tura bakin haure ta hanya daya zuwa can ya sabawa doka.

Sabuwar dokar ta kuma baiwa ƴan majalisar dokoki kan neman mafaka ikon yin watsi da sashin dokar kare hakkin ɗan adama na kasa da kasa da na cikin gida.

Jam'iyyun adawa a Birtaniya da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin ɗan adama daban-daban sun soki manufofin gwamnatin Firayiminista Rishi Sunak mai ra'ayin mazan jiya.

A makon da ya gabata ne ya ce, Jirage za su soma jigilar daukar bakin-hauren wanda za a shafe makonni 10 zuwa12 ana yi.

AFP