A 2014, Bassirou Diomaye Faye ya kafa jam’iyyar Pastef ta ‘Ƴan Kishin Afirka./ Hoto: Reuters

An haifi Diomaye Faye a ranar 25 ga Maris na 1980, a ƙauyen Ndiaganiao da ke yankin Thies na ƙasar Senegal.

Ya yi karatun digiri na biyu a fannin shari’a, kuma ya gama digirin farko a Makarantar Ƙasa ta Nazarin Gudanarwa da Mulki. A 2007 ya fara aiki da Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa.

A 2014, ya kafa jam’iyyar Pastef ta ‘Ƴan Kishin Afirka.

An kama shi a ranar 14 ga watan Afrilun 2023 tare da zarginsa da laifin “daƙile ayyukan jami’an tsaro” bayan ya yi watsi da tsarin shari’ar da aka bi wajen hukunta uban gidansa Ousmane Sonko.

Sakamakon yadda ba a taɓa tuhumar sa da aikata babban laifi, ko gurfanar da shi a gaban kotu ba, ya samu damar tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Diomaye Faye, wanda jama’a ba su san shi sosai ba har zuwa shekara ɗaya da ta gabata, ya samu farin-jininsa ne bayan gallaza wa jam’iyyarsa ta Pastef da aka yi a baya-bayan nan, amma kuma abin da ya fi ɗaga martabarsa shi ne yadda madugun ƴan adawar Senegal Ousmane Sonko ya ce a zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Masu sanya idanu sun bayyana cewa nasarar Diomaye Faye (Da jam’iyyarsa) wata girgizar ƙasa ce ta siyasa kuma za ta sanya a sauya tunani a harkokin siyasar ƙasar.

Faye na kallon kansa a matsayin ɗan takarar kawo sauyi da kishin Afirka baki daya.

Manufofinsa sun haɗa da dawo da martaba da ƙimar Senegal, wadda ya ce an sayar wa ƴan ƙasar waje ita.

Ya kuma yi alƙawarin yaƙar cin hanci da rashawa, tare da raba arzikin ƙasa a tsakanin jama’a.

Faye ya kuma yi alƙawarin sake duba yarjejeniyoyin haƙar ma’adanai, iskar gas da albarkatun man fetur a ƙasar da ta shirya fara haƙo mai da gas a ƙarshen shekarar nan ta 2024.

Ƙasashen duniya sun sanya idanu sosai kan zaɓen na Senegal, wanda ya zo bayan tashin-tashinar siyasa ta tsawon shekara uku a ƙasar da take ɗaya daga mafi zaman lafiya a Afirka.

Senegal ƙasa ce da ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Yammacin duniya a lokacin da Rasha ke ƙoƙarin ƙara saita kanta a yankin ta hanyar ƙulla ƙawance da ƙasashen Sahel.

TRT Afrika da abokan hulda