Kasashen ECOWAS na fuskantar kalubale da dama, daga ciki har da juyin mulki a wasu kasashen yankin. / Hoto: BAT

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kungiyar Sahel Alliance da wasu kasashen Yammacin Afirka suka yi ba zai karkatar da hankalin ECOWAS daga ayyukan da take yi ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin taron kungiyar Shugabannin ECOWAS karo na 64 wanda aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi.

A kwanakin baya ne kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar wadanda ke karkashin mulkin soja suka kafa kungiyar ta Sahel Alliance wadda suka kira da yarjejeniyar Liptako-Gourma.

“Da alama wannan hadakar an yi ta ne da niyyar karkatar da hankalinmu daga abin da muka yarda da shi da ayyukan da muke yi na tabbatar da dimokuradiyya da kyakkyawan shugabanci wanda zai iya tasiri a rayukan jama’a.

“Ba za mu bari a karkatar da hankalinmu ba daga cika burin da muka kudiri aniyar cimma da kuma bin kyakkyawar turba ta hada kan kasashen ECOWAS kamar yadda aka tsara a kundin tsarin kungiyar,” in ji Shugaban na ECOWAS Bola Ahmed Tinubu.

Shugaba Tinubu ya kara jaddada cewa duk da irin kalubalen da yankin na Yammacin Afirka ke fuskanta, ECOWAS ta samu babbar nasara ta bangaren ci gaban yankin.

Kungiyar ta ECOWAS tana fuskantar matsaloli da dama a wannan lokaci, daga ciki har da batun juyin mulki da tsaro da matsin tattalin arziki.

An fuskanci juyin mulkin soji tun daga shekarun 2020, kama daga Mali zuwa Burkina Faso da Guinea da Nijar.

A watan da ya gabata, wani yunkurin juyin mulki a Saliyo ya yi sanadin mutuwar mutum 21, kamar yadda manyan jami’an gwamnatin kasar suka tabbatar a kasar wadda ke cikin kasashen ECOWAS.

Ita ma Guinea-Bissau wadda kasa ce ta ECOWAS, shugabanta Umaro Sissoco Embalo a ranar Asabar ya ce rikicin da aka yi a wannan makon wanda a ciki akwai wasu daga cikin dogaran kasar “yunkuri ne na juyin mulki.”

TRT Afrika