Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace mulki ta hanyar karfin soji a watan Oktoban 2022./ Hoto: Rueters

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore, ya ce ba za a gudanar da zabuka a kasar ba sai lokacin da ta samu zaman lafiya yadda kowa zai iya kada kuri’arsa.

Ya bayyana haka ne ranar Juma’a kwanaki kadan bayan gwamnatin kasar ta kama wasu mutane da ta yi zargin sun yi yunkurin juyin mulki.

Yau shekara guda kenan da Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace mulkin kasar daga hannun gwamnatin Paul Henri-Damiba, wanda shi ma juyin mulki ya yi wa shugaban Burkina Faso a watan Janairun 2022.

Traore ya yi alkawarin gudanar da zaben da zai dawo da mulkin farar-hula a 2024.

Amma a jawabin da ya yi wa 'yan kasar, ya ce tsaron kasar shi ne babban abin da ya sanya a gaba, ko da yake ya kara da cewa yana shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

Labari mai alaka: An dakile yunkurin 'juyin mulki' a Burkina Faso

"Zabe ba shi ne muhimmin abin da ke gabanmu ba, ina so na shaida muku cewa tsaro shi ne babban abin da muke son tabbatarwa" a kasar da ke fama da hare-haren masu tayar da kayar baya.

Duk da haka, ya ce babban burinsa shi ne ya gudanar da zabe, amma bai bayyana lokacin da zai yi hakan ba.

"Ba za a yi zaben da zai mayar da hankali kawai a Ouagadougou da Bobo-Dioulasso da sauran garuruwan da ke kusa ba," in ji shi, yana magana ne a kan yankunan da ba kasafai suke fuskantar hare-haren masu ikirarin jihadi ba.

"Ya kamata dukkan ‘yan Burkina Faso su zabi shugaban kasarsu."

Traore ya yi jawabin ne a yayin da daruruwan ‘yan kasar suka yi gangamin goyon bayansa a babban birninsu a yayin da yake cika shekara guda da juyin mulki.

Magoya bayansa sun taru a babban filin Place de la Nation da ke Ouagadougou suna daga tutocin kasar tare da hotunan Traore.

Ranar Laraba gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta ce ta murkushe wani yunkuri da wasu sojoji da jami'an tsaro suka yi na kifar da gwamnatin kasar.

Hakan na faruwa ne a yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren masu tayar da kayar baya da ke da alaka da Al Qaeda da Islamic State.

Wadannan kungiyoyi sun addabi Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar, abin da ya sa a watan da muke ciki kasashen suka kafa kungiyar Sahel Alliance da zummar hada gwiwa don fatattakar su.

TRT Afrika da abokan hulda