An daure sawun kafar wata mata da ake zargin tana fama da lalurar ciwon hauka da kaca da kwado a wani sansanin addu’a da ke yankin gabashin Ghana, Oktoba 2023. Ta ce, “Ina kwana da sarkar kacan a kafata. Ba na jin dadi.” Hoto: Elizabeth Kamundia /Human Rights Watch  

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani sabon rahoto da ya yi nuni kan yadda ake ci gaba da ɗaure mutane masu fama da larurar ƙwaƙwalwa a Ghana, duk da dokar haramci da gwamnatin kasar ta yi kan wannan mummunar dabi'a a shekarar 2017.

A ziyarar da ƙungiyar ta kai wasu cibiyoyin ba da magani guda biyu - da aka fi sani da "sansanin addu'o'i "- da ke yankin gabashin Ghana a ranar 19 zuwa 23 ga watan Oktoban shekarar 2023, ta zanta da mutane fiye da 30 kan wannan batu.

Daga ciki akwai mutanen da ke fama da larurar ƙwaƙwalwa da kuma ma'aikatan sansanonin da kuma masu ba da shawara kan lafiyar ƙwaƙwalwa da wani ƙwararre kan lafiyar ƙwaƙwalwa da wani babban jami'in gwamnati.

Sai dai rahoton ya gano cewa gwamnati kasar ba ta samar da isassun hanyoyin aiwatar da wannan doka ba, wadanda za su sa ido kan cibiyoyin ba da magani wadanda akasari suke tsare mutane tare da azabtar da su da sunan samar musu waraka.

Kungiyar ta gano wasu mutane goma a cikin sansanonin biyu da aka daure da sarka ba tare da son ransu ba, cikin wani yanayi da kara musu kunci da take musu ƴanci da kuma cin zarafinsu.

"Dokar hana daurin da gwamnatin Ghana ta sanya a shekarar 2017 da kuma alkawuran magance wannan cin zarafi bai kawo karshen daure masu lalurar lafiyar kwakwalwa da nakasa ba," a cewar mataimakiyar daraktan kare hakkin masu fama da nakasa ta kungiyar Elizabeth Kamundia.

“Gwamnati tana bukatar aiwatar da dokar tare samar da hanyoyin taimaka wa mutane don a inganta rayuwarsu, garƙame mutum daya tamkar goma ne,” in ji Elizabeth.

Kungiyar Human Rights Watch ta bayyana cewa ga irin yadda ake matukar take hakkin ɗan'adam a sansanonin biyu, wadanda suka hada da hana abinci da rashin tsafta wurin da rashin samun kulawa ta lafiya da hana walwala da kuma 'yancin yin motsi.

TRT Afrika