Ɗaya daga cikin matasan nan uku waɗanda ake zargi da haddasa gobara a wani gida a Denver wanda gobarar ta kashe ƴan gida ɗaya mutum biyar – an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 40 a gidan yari.
A lokacin da lamarin ya faru, ana zargin matasan sun haddasa gobarar ne domin ramuwar gayya kan wata waya da aka sace wadda a kan kuskure aka bibiye ta zuwa gidan.
Gavin Seymour mai shekara 19 ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa na hannu a kisan kai a ranar 5 ga watan Agustan 2020, inda suka haddasa wata gobara da ta kashe wasu ƴan ƙasar Senegal biyar waɗanda ƴan gida ɗaya ne.
Alƙalin Gundumar Denver Karen Brody ya yanke masa hukuncin ɗauri mafi tsauri a ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Denver Post ta ruwaito.
Kyamarorin tsaro
Ana tuhumar Seymour da wasu matasa biyu - Kevin Bui da Dillon Siebert - da laifin haddasa gobara da tsakar dare, inda suka kashe 'yan uwa waɗanda ƴan gida ɗaya ne da suka haɗa da Djibril Diol mai shekara 29 sai Adja Diol mai shekara 23 da Khadija Diol mai shekara ɗaya da Hassan Diol mai shekara 25 da Hawa Baye mai wata shida.
Wasu mutum uku da ke cikin gidan sun tsira bayan sun tsallaka daga hawa na biyu na ginin.
Sibert wanda a lokacin da aka yi gobarar shekararsa 14 da haihuwa, zuwa yanzu da aka yanke hukuncin ya cika shekara 17 inda aka yanke masa hukunci a watan Fabrairu na shekara uku a gidan yarin yara sai kuma shekara bakwai a gidan yarin matasa.
Seymour da Bui waɗanda ake zargi da jagorantar kisan, suna da shekara 16 a lokacin da lamarin ya faru. Lamarin Bui wanda yake fuskantar zarge-zarge da dama kan hukuncin kisa ba a kammala shari’ar ba.
An kwashe watanni ana binciken gobarar ba tare da samun wata alkibla ba. Fargabar cewa gobarar ta kasance nuna kyama ne ya sa yawancin bakin haure 'yan kasar Senegal sanya na'urorin tsaro a gidajensu ko da an kai musu hari.
‘Babu adalci zuwa yanzu’
“Ko da tumaki ko awaki biyar ka kashe, ya kamata a yi maka ɗauri iya dauri,” in ji Hanady Diol wadda dangin waɗanda aka kashe ne kamar yadda take shaida wa kotu a ranar Juma’a ta hanyar mai tafinta ta wayar tarho daga Senegal.
“Wannan mutumin, suna batun shekara 40 zuwa 30. Hakan na nufin babu adalci a nan. Hukuncin yana nuna kamar mutanen da suka mutu ba bil’adama bane.”
An bayyana yaran a matsayin wadanda ake zargi ne bayan da ‘yan sanda suka samu takardar neman bincike da ke neman Google ya shaida musu mutanen da suka yi bincike kan adireshin gidan cikin kwanaki 15 da faruwar gobarar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.