Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Nijeriya ta bayar da umarni ga manyan jami’anta su tsaurara tsaro a makarantun firamare da sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun sace ɗalibai kusan 300 a Kaduna da kuma sace ɗalibai aƙalla 15 a Sokoto.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Talata ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar CP Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarni ga kwamandojin ƴan sanda da DPO-DPO da ke faɗin jihar su tsaurara tsaro a makarantun.
"A kan haka ne kwamishinan ‘yan sandan ya umarci kwamandojin ƴan sanda da ke aiki da DPO-DPO su ƙara kaimi tare da mayar da hankali wurin sintiri a kewayen dukkan makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare da ke cikin barazana a faɗin jihar," in ji sanarwar.
“An ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaro ga ɗalibai da malamai da sauran ɓangarorin ilimi a jihar. Manufar ƙara jami'an ƴan sanda a waɗannan wurare ita ce daƙile aikata laifuka da samar da ingantaccen yanayi mai dacewa don koyo da koyarwa,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
Matsalar tsaro na yin ƙamari musamman a arewacin Nijeriya inda a ƴan kwanakin nan ƴan bindig suke kai hare-hare da dama.
Domin ko a tsakar daren Litinin sai da ƴan bindigar suka sace aƙalla mutum 61 a ƙauyen Buda da ke Jihar Kaduna.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya bai wa jami'an tsaron ƙasar umarni su "gaggauta" kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Sai dai masu sharhi kan sha'anin tsaro irin su Audu Bulama Bukarti, sun ce muddin gwamnati ba ta tashi tsaye ba, rashin tsaro a arewacin Nijeriya zai fi ƙarfinta.
"Ƴan bindiga sun mamaye ɗaruruwan ƙauyuka a arewa maso yammacin Nijeriya, inda suka maye gurbin gwamnati da masu sarautun gargajiya. A wannan hali da ake ciki, ba za a daɗe ba za su soma ƙwace ikon dukkan ƙananan hukumomi... Dole gwamnatin tarayya ta ɗauki babban mataki kuma nan-take don magance wannan matsala," in ji Bukarti a saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.